NNPC Ta Kulla Yarjejeniya da Kamfanonin China Don Farfaɗo da Matatun Mai

Kamfanin Mai na Ƙasa, wato NNPC Limited, ya rattaba hannu kan wata sabuwar yarjejeniya da kamfanoni biyu daga ƙasar China domin hanzarta gyaran da kuma sake fara aiki na matatun mai na Port Harcourt da Warri.

An sanya hannu kan yarjejeniyar ne a matsayin Memorandum of Understanding (MoU) tare da kamfanonin Sanjiang Chemical Company Limited da Xingcheng (Fuzhou) Industrial Park Operation and Management Co. Ltd a birnin Jiaxing na ƙasar China a ranar 30 ga Afrilu, 2026.

NNPC ta bayyana cewa wannan haɗin gwiwa wata muhimmiyar nasara ce a yunƙurin sauya fasalin matatun mai, inda za a daina tsarin ɗaukar ‘yan kwangila kawai, a koma tsarin haɗin jari da fasaha, inda dukkan ɓangarori za su raba haɗari da riba.

Babban Daraktan Kamfanin (Group CEO), Bashir Bayo Ojulari, ya ce:
“Dukkan ɓangarorin sun fahimci akwai damar cin gajiyar juna wajen bunƙasa matatun mai na NNPC a Najeriya tare da tabbatar da dorewar ribar su a nan gaba.”

Yarjejeniyar ta ƙunshi kammala sauran ayyukan gyara a matatun, gudanarwa da kula da su domin tabbatar da ingantaccen aiki, da kuma faɗaɗa su domin samar da man fetur mai tsafta da sinadarai na petrochemical. Haka kuma, an tsara samar da cibiyoyin masana’antu masu amfani da iskar gas kusa da matatun.

Ojulari ya jaddada cewa sabon tsarin zai tabbatar da gaskiya da ɗaukar alhaki, yana mai cewa:
“Zamanin kashe biliyoyin kuɗi wajen gyara matatun mai ba tare da samun sakamako mai dorewa ba ya ƙare. Yanzu muna mai da hankali kan haɗin gwiwa da ke kawo ƙima, fasaha, da ingantaccen aiki.”

Matatar mai ta Port Harcourt mai ƙarfin tace ganga 210,000 a rana ta taɓa fara aiki a ƙarshen shekarar 2024 bayan gyaran dala biliyan 1.5, amma aka sake rufe ta a watan Mayu 2025. Ita kuwa matatar Warri mai ƙarfin ganga 125,000 a rana na ci gaba da gyaranta a wani shiri na dala miliyan 897.

NNPC ta ce sabon haɗin gwiwar na da nufin buɗe cikakken damar ɓangaren tace mai na Najeriya, rage dogaro da shigo da mai daga ƙasashen waje, da haɗa harkar tace mai da petrochemical da amfani da iskar gas domin samar da “ainihin darajar tattalin arziki.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *