Trends

NAFDAC Ta Fara Aiwatar da Haramcin Giya Cikin Sachet

Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa (NAFDAC) ta fara aiwatar da haramcin samarwa da sayar da giya a cikin sachet da kuma kwalaben PET da ke ƙasa da mililita 200.

Daraktar Janar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da hukumar ta shirya a ranar Laraba a Lagos.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa (NAN) ya ruwaito cewa NAFDAC ta sanar a ranar 11 ga Nuwamba, 2025, shirinta na aiwatar da cikakken haramcin irin waɗannan kayayyaki zuwa Disamba 2025, bisa umarnin Majalisar Dattawan Ƙasa.

Sai dai an dakatar da aiwatar da haramcin a wancan lokaci, bayan da Gwamnatin Tarayya ta bayar da umarnin dakatar da duk wasu matakai da ayyuka da suka shafi shirin haramcin, har sai an kammala tattaunawa da fitar da umarni na ƙarshe.

Adeyeye ta ce yanzu hukumar ta karɓi umarnin da ya dace daga Majalisar Dattawa don ci gaba da aiwatar da haramcin, kuma tuni aka fara aiwatarwa.

Ta bayyana cewa haramcin na da nufin kare lafiyar al’umma da kuma kariya ga masu rauni, musamman yara, matasa da samari, daga illolin shan giya.
“Yawaitar giya mai yawan sinadarin barasa a cikin sachet da ƙananan kwalabe ya sa kayayyakin suke da sauƙin samu, araha, kuma ana iya ɓoye su cikin sauƙi,” in ji ta.

“Mun riga mun fara aiwatar da haramcin samar da giya a sachet da kwalaben da ke ƙasa da mililita 200, bayan mun karɓi umarni daga Majalisar Dattawa.

“NAFDAC ba ta hana shan giya gaba ɗaya ba, amma muna adawa da yaduwar giya mai yawan ƙarfi a cikin sachet da ƙananan kwalabe, domin hana yara samun sauƙin kaiwa gare ta,” in ji Adeyeye.

Ta ƙara da cewa kafin ta hau kujerar shugabar NAFDAC, giya a sachet na ɗauke da kashi 50 zuwa 90 cikin 100 na barasa, abin da ta bayyana a matsayin mai matuƙar haɗari.

“Mun bukaci masana’antu su rage yawan barasar zuwa kashi 30 cikin 100, amma sai suka garzaya ma’aikatar lafiya suna nuna rashin jin daɗinsu, suna cewa hakan zai jawo asarar ayyukan yi da jarin su.

“Tsohon Ministan Lafiya ya ba su wa’adin shekaru biyar, daga Disamba 2018 zuwa 31 ga Janairu, 2024, domin su daidaita harkokin kasuwancinsu,” in ji ta.

Adeyeye ta jaddada aniyar NAFDAC na ci gaba da kare lafiyar ƙasa, musamman lafiyar masu rauni kamar yara, ta hanyar ayyukanta na tsare-tsare da sa ido.