IMPI Ta Yi Hasashen Ci Gaban Tattalin Arzikin da Kashi 5.5 a 2026

Ɗaya daga cikin fitattun ƙungiyoyin ba da shawarwari kan manufofi a Najeriya, wato Independent Media and Policy Initiative (IMPI), ta yi hasashen cewa tattalin arzikin ƙasar zai bunƙasa da kashi 5.5 cikin 100 a shekarar 2026, bisa sabon tsarin tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta runguma.

A cikin wata sanarwar manufofi da Shugabanta, Dokta Omoniyi Akinsiju, ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta ce wannan hasashe ya zarce na Bankin Duniya da Asusun Ba da Lamuni na Ƙasa da Ƙasa (IMF), tare da nuna ƙara samun amincewa da sabon tsarin tattalin arzikin da Najeriya ke aiwatarwa.

IMPI ta danganta wannan hasashe da abin da ta kira sauyin salo daga dogaro da kuɗaɗen shigar man fetur da Najeriya ta daɗe tana yi, zuwa sabon tsarin tattalin arziki da ke tafiya bisa manufofi da tsare-tsaren gwamnati domin sauƙaƙa harkokin kasuwanci.

A cewar ƙungiyar, sabon tsarin ya mayar da hankali ne kan amfani da manufofi, dokoki da ginshiƙan hukumomi na gwamnati domin rage cikas, sauƙaƙa farashin mu’amala, da kuma hanzarta ayyukan tattalin arziki, musamman a ɓangaren kasuwanci da zuba jari.

Sanarwar ta ce, “Wannan sauƙaƙa wa tattalin arziki, a wannan ma’ana, na nufin samar da ci gaba mai ɗorewa kuma mai haɗa kowa ta hanyar ƙara inganci da rage yawan shinge da takardu.”

Cibiyar ta lura da cewa IMF ma kwanan nan ta sake duba matsayinta kan tattalin arzikin Najeriya, inda ta ɗaga hasashen ci gaban shekarar 2026 zuwa kashi 4.4 cikin 100, bayan watanni bakwai da IMPI ta bayyana a matsayin hasashe mara gamsarwa da aka yi a baya.

IMPI ta ce wannan sabon hasashen IMF shi ne mafi girma da asusun ya taɓa yi wa Najeriya cikin shekaru 17 da suka gabata, tana mai bayyana hakan a matsayin bayyanannen alamar dawo da amincewa da alkiblar tattalin arzikin ƙasar.

Baya ga IMF, ƙungiyar ta ce yanzu akwai kusan yarjejeniya tsakanin masu sharhi kan tattalin arziki na cikin gida da na ƙasashen waje cewa ci gaban tattalin arzikin Najeriya a 2026 zai haura kashi 4 cikin 100.

Duk da cewa Gwamnatin Tarayya ta yi hasashen ci gaban tattalin arziki da kashi 4.68 cikin 100 a shekarar, IMPI ta ce Ƙungiyar ’Yan Kasuwa da Masana’antu ta Legas (Lagos Chamber of Commerce and Industry – LCCI) ta yi hasashen kashi 7 cikin 100, yayin da Ƙungiyar Taron Tattalin Arzikin Najeriya (Nigeria Economic Summit Group) ta yi hasashen kashi 5.5 cikin 100.

Ta ƙara da cewa kamfanin PwC ya tsaya kan hasashe mai tsaka-tsaki na kashi 4.3 cikin 100, wanda ya dogara da samun hauhawar farashin man fetur, yayin da Bankin Duniya ya ɗaga hasashensa daga kashi 3.7 zuwa kashi 4.4 cikin 100.

IMPI ta bayyana cewa kusantar juna da waɗannan hasashe na nuna fitowar sabon salo na tattalin arziki da ya ta’allaka ne kan ƙara samarwa da ingancin aiki, daidaiton kasuwar canjin kuɗaɗe, rage hauhawar farashi, ingantuwar shigowar jarin waje kai tsaye, da yanayin dokoki da bai cika tsangwama ba.

A cewar ƙungiyar, waɗannan sakamako na faruwa ne sakamakon manufofin sauƙaƙa tattalin arziki da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa da gangan.