Trends

Gwamnatin Tinubu Ta Fi Fifita Kudu Ta Bar Arewa – Kwankwaso

Bola Ahmed Tinubu Shugaban kasan Nigeriya

Kano, Najeriya – Jagoran siyasar Kano kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya caccaki gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan abin da ya bayyana a matsayin rashin adalci wajen rabon arzikin ƙasa, inda ya zargi gwamnatin da fifita ci gaban yankin kudu tare da watsi da arewacin ƙasar.

Kwankwaso, wanda ya kasance ɗan takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar New Nigeria People’s Party (NNPP) a zaben 2023, ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin taron masu ruwa da tsaki na jihar Kano kan gyaran kundin tsarin mulki na 2025.

Ya ce:
“Ina so in ba Gwamnatin Tarayya shawara dangane da rabon arzikin ƙasa. Daga bayanan da muke da su, ya nuna cewa yawancin kasafin kuɗin ƙasa yanzu yana karkata zuwa bangare guda na ƙasa.”

Kwankwaso ya zargi jam’iyyar mai mulki ta All Progressives Congress (APC) da nuna bangaranci wajen rabon albarkatu, yana mai cewa hakan na daga cikin dalilan da ke haddasa matsaloli irin su tsaro, talauci da kuma koma bayan da ake fama da su a yankin arewa.

“Wadanda ke kokarin kwashe komai su sani cewa wasu daga cikin matsalolin da muke fama da su a nan sun samo asali ne daga rashin isasshen albarkatu da kuma barnatar da ƙalilan da ake samu,” in ji shi. “Wannan ne ya haifar da rashin tsaro da talauci da sauran su. Kodayake yana faruwa ne a nan Arewa, kamar hamada, zai bazu zuwa ko’ina.”

Ya bayyana takaicin yadda hanyoyin motoci a Arewa ke ci gaba da lalacewa ba tare da kulawa daga gwamnati ba, yayin da gwamnati ke ware makudan kudade don gina ababen more rayuwa a Kudu.

“Jiya ina so in zo ta jirgin sama, amma kamfanin jirgin ya sauya lokacin tashin daga 3 na rana zuwa 8 na dare. Sai na yanke shawarar zuwa ta hanya. Daga Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano, hanya ce ta azaba. Matukar muni. Wannan hanya an fara ta tun da APC ta hau mulki, amma har yanzu ba a gama ta ba.

“Yanzu muna jin cewa akwai wata babbar hanya daga Kudu zuwa Gabas. Muna maraba da duk wani ci gaba a kowane yanki na ƙasar nan… amma ainihin abin da ba daidai ba ne shi ne gwamnatin da ke daukar dukiyar kasa tana jefawa a wuri guda yayin da sauran yankuna ke zama cikin koma baya.”

Kwankwaso ya bukaci gwamnatin Tinubu da ta sake fasalin tsarin raba albarkatu domin tabbatar da adalci da daidaito ga kowanne yanki na ƙasar.

“Yanzu ne lokacin da gwamnati za ta tabbatar wa da jama’a cewa ba ta tsaya gefe guda ba,” in ji Kwankwaso.

Rahoton: Channels TV