Gwamnatin Tarayya ta amince da kashe naira biliyan ₦6 domin gina manyan makarantu uku (mega schools) a Jihar Gombe, a cewar Ministan Bunƙasa Yankuna, Alhaji Uba Ahmadu.
Ministan ya bayyana hakan ne a garin Kumo, Ƙaramar Hukumar Akko, yayin ƙaddamar da ɗakin kwanan ɗalibai mai gadaje 250 da Hukumar Raya Arewa maso Gabas (NEDC) ta gina. Ya ce makarantu ukun na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin sauƙaƙa samun ilimi da kuma ƙara gasa a fannin ilimi a yankin.
An gina makarantu ukun ne a Dadin Kowa (Gombe Ta Tsakiya), Dukku (Gombe Arewa) da Kaltungo (Gombe Kudu) na mazabun Sanata, duk ƙarƙashin kulawar NEDC.
Ahmadu ya jaddada cewa wannan shiri na da nufin cike gibin ilimi tsakanin yankin Arewa maso Gabas da sauran sassan Najeriya.
“Gwamnatin tarayya na mai da hankali wajen samar da muhallan koyo na zamani da ke zaburar da ɗalibai tare da inganta sakamakon karatu,” in ji shi.
Ministan ya ƙara da cewa makarantu sun samu muhimman kayayyakin more rayuwa, ciki har da masaukin ɗalibai mai kyau, wanda a cewarsa zai taimaka wajen ƙara nutsuwa da kyakkyawan aiki a karatu ta hanyar samar da yanayi mai tallafawa ɗalibai.
Ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Gombe bisa haɗin gwiwar da ta yi da NEDC, yana mai bayyana wannan haɗin gwiwa a matsayin abin koyi wajen ci gaban ilimi mai ɗorewa da bunƙasar yankuna.
Manyan makarantu (mega schools) a Najeriya su ne manyan cibiyoyin ilimi na zamani da ke ɗauke da dakunan gwaje-gwajen ICT, dakunan karatu da azuzuwa, waɗanda galibi ake nufin su samar da ingantaccen muhallin koyo ga dubban ɗalibai, ciki har da ’yan gudun hijira a cikin gida (IDPs) da marayu.
