Gwamnan Gombe Ya Sanya Hannu Kan Dokar Kafa Sabbin Yankuna ci Gaba

Inuwa Yahaya Gwamnan Jihar Gombe

Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, a jiya ya sanya hannu kan kudirin dokar kafa sabbin Kananan Hukumomi na Ci Gaba (LCDAs) guda 13 daga cikin Kananan Hukumomi 11 da ake da su a jihar.

Tun makonni biyu da suka gabata ne gwamnan ya mika wannan kudiri ga majalisar dokokin jihar domin neman amincewarta.

Da yake jawabi jim kaɗan bayan sanya hannu kan kudirin a fadar gwamnatin jihar, Gwamna Yahaya ya bayyana cewa kafa sabbin LCDAs zai sauƙaƙa tafiyar da mulki tare da kusantar da gwamnati ga al’umma.

Ya ce hakan zai kawo sabon salo na ci gaba ga al’ummomin da abin ya shafa da kuma jihar baki ɗaya.

Gwamnan ya umurci sabbin LCDAs da su mayar da hankali wajen inganta tsaro, ilimin boko na farko, kiwon lafiyar farko, da kuma noma – sassan da ya bayyana a matsayin ginshiƙan ci gaban al’umma a matakin ƙasa.

Don tabbatar da sauƙin sauya sheka daga tsofaffin kananan hukumomi zuwa sabbin LCDAs, Gwamnan ya sanar da kafa kwamitocin rikon kwarya na wucin gadi, tare da tsarin aiwatarwa a matakai domin tabbatar da ingantacciyar tafiya tun daga farko.

Haka zalika, ya kafa kwamitin fasaha mai mutum 10 karkashin jagorancin mataimakin gwamnan, Dakta Manassah Daniel Jatau, tare da haɗa kwamishinan shari’a, kwamishinan harkokin kananan hukumomi, kwamishinan kudi, shugaban hukumar ayyukan kananan hukumomi, shugabannin ALGON na jihar, darakta-janar na hukumar ayyukan hadin gwiwa, mai binciken asusun kananan hukumomi, da shugaban NULGE na jihar. Babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi kuma shi ne zai rike matsayin sakatare.

A cewarsa, babban aikin wannan kwamitin shi ne tabbatar da sauya mulki cikin sauƙi daga manyan kananan hukumomi zuwa sabbin LCDAs ba tare da katse muhimmancin ayyukan gwamnati ga jama’a ba.

Sabbin LCDAs da aka amince da su da cibiyoyinsu sun haɗa da:

Akko Arewa (Amada),

Akko Yamma (Pindiga),

Balanga Kudu (Bambam),

Billiri Yamma (Tal),

Dukku Arewa (Malala),

Funakaye Kudu (Tongo),

Gombe Kudu (Bolari),

Kaltungo Gabas (Wange),

Kwami Yamma (Bojude),

Nafada Kudu (Birin Fulani),

Pero-Chonge (Filiya),

Yamaltu Gabas (Hinna),

Yamaltu Yamma (Zambuk).