An yi bikin zagayowar ranar haihuwar Shugabar Nigeria Union of Journalists ta FCT, Grace Ike, a yau 24 ga Maris, 2026, inda mambobin ƙungiyar, ƙungiyoyin mata da dama, da sauran abokan hulɗa suka bayyana ta a matsayin jagora mai kawo sauyi a fannin aikin jarida.
Masu taya ta murna sun yabawa Grace Ike bisa yadda ta karya katangar da ke hana mata samun manyan muƙamai, bayan da ta zama mace ta farko da aka zaɓa a matsayin Shugabar NUJ FCT bayan sama da shekaru arba’in da kafuwar majalisar.
A cewarsu, tun bayan hawanta kujerar shugabanci, ta aiwatar da ayyuka masu muhimmanci da suka shafi inganta ababen more rayuwa da kuma kula da jin daɗin mambobi, lamarin da ya sanya cigaban ƙungiyar ya samu gagarumin sauyi.
Rahotanni sun nuna cewa a zamanin jagorancinta, an samu gagarumar ci gaba da kuma ƙarfafa haɗin kai tsakanin mambobi, tare da jan hankalinsu su riƙa shiga harkokin ƙungiyar yadda ya kamata.
A sakon taya murna da aka fitar, an bayyana Grace Ike a matsayin “gwarziyar shugaba” wadda take da matuƙar tasiri, tare da yi mata fatan samun ƙarin nasarori, lafiya da arziki a sabuwar shekararta.
Masu fatan sun kuma roƙi Allah Ya ci gaba da ɗaukaka ta, Ya ba ta ikon ci gaba da jagoranci cikin hikima da nasara, har ta kai ga kololuwar burinta a rayuwa.
An kammala sakon da taya ta murna da addu’o’i, inda aka bayyana ta a matsayin “mace mai ban mamaki” wadda ke zama abin koyi ga al’umma.
