Trends

FG ta Kaddamar da Hukumar PenCom Yayin da Kadarorin Fansho ya Naira N28 tln

Gwamnatin Tarayya ta kaddamar da kwamitin gudanarwa na National Pension Commission (PenCom), tare da dorawa mambobinta alhakin kare sama da naira tiriliyan 28 na kadarorin fansho da ke karkashin Tsarin Fansho na Gudummawa.

A wajen bikin da aka gudanar a Abuja, Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya bayyana PenCom a matsayin “ginshiƙi mai muhimmanci a fannin tattalin arzikin Najeriya, wanda aka ɗora masa amanar ajiyar fansho na miliyoyin ‘yan ƙasa.”

Ya jaddada cewa rawar da kwamitin zai taka na da matuƙar muhimmanci ga ƙasa, musamman wajen bayar da jagoranci da kuma sa ido bisa dokar Pension Reform Act 2014, tare da gargadin kada a tsoma baki cikin harkokin gudanarwa na yau da kullum.

Akume ya buƙaci mambobin kwamitin su rungumi tsarin rashin jure wa cin hanci da rashawa, su kuma ƙarfafa hanyoyin sa ido na cikin gida, sarrafa haɗari da kuma tabbatar da gaskiya da riƙon amana.

Ya ce, “Ayyukan kwamitin dole ne su ƙarfafa amincewar jama’a ga tsarin fansho, tare da tabbatar wa masu bayar da gudummawa cewa ajiyarsu na cikin tsaro kuma ana sarrafa ta yadda ya dace.”

Ya ƙara da cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu na da kudurin cika alƙawuran fansho, magance basussuka, da kuma tabbatar da cewa masu ritaya na karɓar hakkokinsu cikin mutunci, tabbaci da kuma a kan lokaci.

Shugaban kwamitin, Opeyemi Agbaje, ya yi alƙawarin gudanar da aiki cikin gaskiya da shugabanci mai ƙarfi, yana mai cewa za a yi amfani da kudaden fansho wajen bunƙasa ƙasa a fannoni kamar ababen more rayuwa da gidaje.

Babbar Daraktar PenCom, Omolola Oloworaran, ta bayyana kaddamarwar a matsayin mai muhimmanci kuma ta dace da lokaci, domin ta dawo da cikakken tsarin sa ido bayan wani lokaci ba tare da kwamitin gudanarwa ba. Ta kuma jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin shugabanci da ma’aikata domin samar da alfanu ga masu ajiya da masu ritaya.

Masu ruwa da tsaki sun bayyana kwarin gwiwa cewa ingantaccen shugabanci da gaskiya za su ƙara ƙarfafa masana’antar fansho ta Najeriya, wadda ta ci gaba da bunƙasa har ta kai sama da naira tiriliyan 28 a kadarori.