CBN Ta Soke Bukatar Rantsuwar Kotu Don Asusun Banki Marasa Aiki

Yemi Cardoso Shugaban babban Bankin Najeriya wato CBN

Babban Bankin Najeriya (CBN) ta sabunta dokokinta kan asusun banki marasa aiki, inda ta soke wajibcin gabatar da takardar rantsuwar kotu (affidavit) ga kwastomomi da ke son sake kunna irin wadannan asusu.

A cikin wata sanarwa da aka fitar ranar 12 ga Maris, 2026, wadda Rita Sike ta sanya wa hannu, bankin ya ce an dauki wannan mataki ne bayan shawarwari da masu ruwa da tsaki, domin saukaka wa jama’a samun kudaden su tare da ci gaba da kiyaye tsaro.

Sanarwar ta ce an soke tanadin da ke karkashin Sashe na 8.0(ii), wanda ya tilasta amfani da takardar rantsuwar kotu wajen sake kunna asusun da ya daina aiki.

Sai dai CBN ta bayyana cewa wannan sassaucin ya shafi asusun da ba a kai kudaden su zuwa Unclaimed Balances Trust Fund (UBTF) ba. Ga asusun da aka riga aka mayar da kudaden su zuwa asusun UBTF, har yanzu dole ne a gabatar da affidavit.

Haka kuma, bankuna da cibiyoyin kudi za su ci gaba da yin cikakken bincike (due diligence) domin tabbatar da sahihancin bayanan kwastomomi kafin sake kunna asusun.

Sabuwar dokar ta kuma wajabta wa bankuna su rika wallafa jerin asusun da ba su aiki da kudaden da ba a karba ba a shafukan yanar gizon su da kuma a kalla jaridu biyu na kasa a duk shekara. Bayanan da za a fitar sun hada da sunan mai asusu, nau’in asusu, sunan banki, da adireshin reshe.

CBN ta bayyana cewa wannan tsarin bayyanawa ya yi daidai da dokar kare bayanan sirri ta Najeriya da kuma dokar Banks and Other Financial Institutions Act 2020 (BOFIA 2020), wadda ta bai wa bankin ikon kula da kudaden da ba a karba ba.

Sabuwar dokar ta maye gurbin wadda aka fitar a ranar 17 ga Fabrairu, 2025, kuma ta fara aiki nan take, a matsayin wani yunkuri na CBN na kara inganta gaskiya da saukaka wa jama’a samun kudaden su a tsarin banki.