Trends

Ban Taɓa Cewa Zan Janye wa Kowa ba — Atiku

Atiku Abubakar Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya karyata rahotannin da ke cewa ya yi alƙawarin janye takararsa ta 2027 domin ba wani matashi dama ya tsaya.

Mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya fitar da sanarwa inda ya ce wasu kafafen yaɗa labarai sun yi wa maganganun Atiku a tattaunawarsa da BBC Hausa mummunan fassara.

Ibe ya bayyana cewa bayan an duba bidiyo da rubutaccen bayani na hirar, ba a samu inda Atiku ya fito fili ya faɗi ko ya nuna cewa zai janye wa wani ba.

Ya ce abin da Atiku ya yi magana a kai kawai shi ne cewa matasa da sauran ‘yan takara su ji daɗin shiga takarar shugabanci.

Sai dai kuma, Ibe ya ƙara da cewa Atiku ya bayyana shirinsa na marawa matashi baya idan ya fito daga tsarin sahihin zaɓen fitar da ɗan takara.

Sanarwar ta yi kira ga kafafen yaɗa labarai da su guji yin fassarar da za ta haifar da rudani, inda ta bayyana cewa irin waɗannan rahotanni ba su dace da abin da aka faɗa ba.

A cewarsa, maganganun da ake yadawa cewa Atiku zai janye takara domin wani matashi ba daidai ba ne, kuma ba su yi daidai da manufar Atiku ba.

Sanarwar ta kuma jaddada cewa a hirar da aka yi da shi, Atiku ya karfafa matasa su shiga siyasa, amma bai taɓa cewa zai bar wa wani gurbi ba.

Tun da farko wasu rahotanni sun ruwaito cewa Atiku zai iya janye muradinsa na takarar shugaban ƙasa domin tallafa wa wani matashi, bisa ga abin da suka ce ya fito daga hirarsa da BBC Hausa.