Trends

AFCON 2025: Super Eagles ta Doke Masar, ta Lashe Matsayi na Uku

Ƙungiyar kwallon ƙafa ta Najeriya, Super Eagles, ta kawar da bakin cikin rashin sa’a a bugun fanareti bayan da ta doke Masar a bugun daga kai sai mai tsaron gida, inda ta lashe lambar tagulla (matsayi na uku) a gasar cin kofin nahiyar Afirka ta 2025.

Super Eagles ta sha kashi a hannun mai masaukin baki, Morocco, a wasan kusa da na ƙarshe ta hanyar bugun fanareti.
A wasan da ta fafata da Masar, wadda ake kira Fir’auna, an kasa samun ƙwallo a cikin mintuna 90 na wasan, lamarin da ya sa aka tafi kai tsaye zuwa bugun fanareti, ba tare da ƙarin lokaci ba.

A bugun fanaretin, mai tsaron ragar Najeriya, Stanley Nwabali, ya zama gwarzo bayan da ya hana Mohamed Salah da Omar Marmoush cin ƙwallo.

A ƙarshe, Najeriya ta yi nasara da ci 4–2 a bugun fanareti, inda ta lashe lambar tagulla karo na tara, wanda ya zama mafi yawa a tarihin gasar.

Ana sa ran buga wasan ƙarshe na gasar gobe tsakanin Morocco da Senegal.