Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) ta janye yajin aikin da ta fara a ranar 29 ga Yuli, 2025, domin neman karin albashi, kyautata walwala, da inganta yanayin aiki a cibiyoyin lafiya na gwamnatin tarayya.
Ministan Lafiya, Farfesa Ali Pate, ne ya bayyana hakan ga manema labarai bayan wata ganawa a bayan-kofa da shugabannin kungiyar da aka yi a ranar Juma’a da rana.
A cewarsa, an cimma matsaya tare da shugabannin kungiyar wanda ya kai ga janye yajin aikin.
Sai dai shugabannin kungiyar sun ki yin tsokaci ga manema labarai bayan kammala taron da aka gudanar a sirrance.
A baya, kungiyar ta fara yajin aikin gargadi tun daga ranar 29 ga Yuli, bayan gwamnatin tarayya ta gaza cika sharuddan wa’adin kwanaki 15 da suka gindaya mata tun daga ranar 14 ga Yuli, 2025.
Yajin aikin ya shafi ma’aikatan jinya a asibitocin gwamnati a fadin kasar, kuma ana sa ran zai dore har zuwa 5 ga Agusta, 2025, idan ba a cimma matsaya ba.
Dalilan yajin aikin sun hada da koke-koken da suka dade suna yi kan rashin kulawa ga jin dadinsu da kuma mummunan yanayin da suke aiki a ciki.
Kungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta:
Kara adadin kudin aiki a lokaci na musamman (shift allowance)
Sake duba kudin kayan aiki da kaya na ma’aikata (uniform allowance)
Kaddamar da sabon tsarin albashi na musamman ga ma’aikatan jinya
Kara yawan kudin aikin yau da kullum (core duty allowance)
Daukar sabbin ma’aikatan jinya da yawa
Kirkirar sashen musamman na ma’aikatan jinya a Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya
Shugaban kungiyar na kasa, Malam Morakinyo Rilwan, ya ce gwamnati ta gaza yin mu’amala da kungiyar cikin wa’adin da aka basu.
“Gaskiya babu wata tattaunawa daga gwamnati har yanzu. Wannan ne ya sa muka ce yajin aiki zai ci gaba, babu abin da zai hana shi. Ko da gwamnati ta kira yau ko gobe, hakan ba zai dakatar da yajin aikin ba. Sun samu isasshen lokaci,” in ji Rilwan.
Ya kara da cewa matakin shiga yajin aikin ba daga shugabannin kungiyar ne kadai ya fito ba, illa wata fitar da zuciya da gajiya daga mambobin kungiyar da suka dade suna kokawa kan halin da suke ciki.
