Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya bayyana cewa Kebbi ce kadai jiha a Najeriya da ke bayar da ilimi kyauta cikin kashi 100 tare da cikakken tallafin karatu ga daliban da ke karatu a cikin gida da kuma kasashen waje.
Gwamna Idris ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar ban girma da Mai Taimakawa Shugaban Kasa na Musamman kan Harkokin Dalibai, Mista Sunday Dare, ya kai masa a gidan gwamnati da ke Birnin Kebbi a ranar Alhamis.
Mista Dare ya samu rakiyar Shugaban Kungiyar Daliban Najeriya (NANS) na kasa, Mista Olusola Oladejo, domin halartar bikin rantsar da sabbin shugabannin kungiyar daliban Kebbi (Kebbi National Students’ Association).
A yayin ganawar, Gwamna Idris ya shaida musu cewa ya biya kusan Naira biliyan 2.7 a matsayin kudin makaranta na daliban da ke karatu a jami’o’i da makarantun gaba da sakandare a cikin gida da kasashen waje.
Ya ce: “Zai baku sha’awa ku sani cewa Kebbi ce kadai jiha a Najeriya da ke bayar da ilimi kyauta baki daya. Muna biyan kudin makaranta daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu. A baya-bayan nan ne na biya Naira biliyan 2.7 don kudin makarantar dalibai a cikin gida da kasashen waje.”
A cewarsa, gwamnatin jihar na bayar da cikakken tallafin karatu ga dukkan daliban jihar Kebbi domin rage wa iyaye nauyin kudin makaranta.
“Wasu iyaye na da yara fiye da uku a manyan makarantu. Idan kudin makaranta ya yi yawa, wasu ba za su iya daukar nauyin ba, musamman a wannan lokaci da makarantun gaba da sakandare da dama suka kara kudin karatu. Wannan ya sa muka yanke shawarar daukar nauyin ilimi da bayar da tallafin karatu ga dukkan dalibanmu,” in ji gwamnan.
Idris ya kara da cewa gwamnatin sa ta ninka kudin ciyarwa na daliban kwana daga Naira miliyan 150 zuwa Naira miliyan 300 a kowane wata.
Domin inganta harkar koyarwa da ilmantarwa, gwamnan ya bayyana cewa an dage takunkumin daukar ma’aikata, inda aka dauki malamai 5,000 da suka cancanta aiki a makarantu.
“Domin kyautata muhalli na koyo, mun gyara makarantu 2,004 na firamare da sakandare, tare da gina sababbin makarantu sama da 340,” in ji shi.
Dangane da ci gaban gine-gine, Gwamna Idris ya yaba wa Shugaban Kasa Bola Tinubu saboda goyon bayan da ya baiwa jihar wajen gina tituna da sauran manyan ayyuka.
Ya jaddada cewa titin Sokoto-Badagry Super Highway mai nisan kilomita 1,008 na daya daga cikin manyan ayyukan gwamnatin Tinubu, inda ya bayyana cewa Jihar Kebbi za ta ci gajiyar gina kilomita 280 cikin titin.
Gwamnan ya kuma gode wa Shugaban Kasa bisa soke kwangilar titin Koko-Zuru mai nisan kilomita 87, yana mai cewa hakan ya baiwa jihar damar karbar aikin da kanta domin kammala shi cikin lokaci, sannan daga bisani gwamnatin tarayya za ta biya.
Gwamna Idris ya kuma yabawa Shugaban Kasa bisa bullo da tsarin lamunin dalibai (students’ loan scheme), wanda ya bayyana cewa wannan shi ne karo na farko da hakan ya faru a tarihin Najeriya. Ya kara da cewa gwamnatin sa tana aiwatar da manufofin Renewed Hope Agenda na shugaban kasa a cikin jihar.
A nasa jawabin, Mai taimakawa shugaban kasa kan harkokin dalibai ya yabawa gwamnatin jihar bisa aiwatar da ilimi kyauta da bayar da tallafin karatu ga dalibai.
Shi kuwa shugaban NANS na kasa ya yaba da gina manyan makarantu guda hudu (mega schools) a fadin masarautu hudu na jihar.
