Ministan Ilimi, Dr. Tunji Alausa, ya sanar da shirin gwamnati na fara aiwatar da gwajin dole da bazata na miyagun kwayoyi ga daliban manyan makarantu a fadin kasar nan.
Wannan sanarwa ta biyo bayan wata ganawa da aka yi a Abuja tsakanin Ministan Ilimi da Shugaban Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA), Manjo Janar Buba Marwa mai ritaya, inda suka tattauna kan hanyoyin dakile yawaitar shan miyagun kwayoyi a tsakanin dalibai.
Alausa ya nuna goyon bayan sa ga dabarun NDLEA na magance matsalar shan kwayoyi ta hanyar amfani da dabaru guda uku: sake duba darussan ilimin miyagun kwayoyi a makarantu, kirkirar shirin wayar da kai kan illar shan kwayoyi a makarantun sakandare, da kuma fara aiwatar da manufar gwajin miyagun kwayoyi a jami’o’i da sauran manyan makarantu. Wannan manufa za ta shafi sabbin dalibai da wadanda suka dawo, tare da gwaje-gwaje bazata a tsawon shekara.
A nasa jawabin, Marwa ya bayyana matsalar shan miyagun kwayoyi a matsayin barazana ga tsaron kasa, yana mai jaddada alakar dake tsakanin amfani da kwayoyi da aikata laifuka irinsu ta’addanci da fashi. Ya bayyana cewa, a cikin shekaru biyu da suka gabata, NDLEA ta kama fiye da masu laifi 40,000 da kuma kama fiye da tan 5,500 na miyagun kwayoyi. “Muna yakar wannan danyen aiki don ceto rayuwar ’ya’yanmu,” in ji shi. “Ba tare da kwayoyi ba, da yawancin laifuka ba za su yiwu ba.”
Ministan Ilimi ya jaddada hakan, yana mai cewa shan kwayoyi na lalata makomar dalibai ta fannin ilimi da tunani. “Idan matasa sun fara shan kwayoyi, ba za su iya zuwa makaranta yadda ya kamata ba, kuma ko da sun je, ba za su samu ingantaccen ilimi ba,” in ji Alausa. “Wannan na rage musu damar yanke shawara mai ma’ana a gaba, wanda hakan ke haifar da matsalar rashin aikin yi da sauran matsaloli na rayuwa.”
Alausa ya bayyana cewa an kafa wani sabon sashi mai suna Substance Use Prevention Unit a cikin ma’aikatar ilimi domin kula da rigakafin amfani da kwayoyi. Ya kara da cewa an fara aikin gyara kundin karatu na makarantun sakandare.
Haka kuma, Ministan ya bayyana cewa ana shirin saka ilimin rigakafin shan kwayoyi tun daga matakin firamare zuwa sakandare. “Muna duba kundin karatun sakandare yanzu. Wannan ne dalilin da ya sa na bukaci Daraktan Makarantun Sakandare ya halarta, domin mu samu hanyar yadda za a shimfida wannan manufa har zuwa matakin firamare,” in ji shi.
Bugu da kari, Ministan ya nemi a kafa kwamitin hadin gwiwa tsakanin Ma’aikatar Ilimi da NDLEA domin tabbatar da nasarar shirin. Ya kuma sha alwashin yin aiki tare da Hukumar Ilimin Firamare ta Kasa (UBEC) da Asusun Tallafawa Manyan Makarantu (TETFund) domin taimakawa Makarantar NDLEA da ke Jos, Jihar Filato.
