Tsohon Sanatan da ya wakilci Kogi ta Yamma, Dino Melaye, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a hukumance.
A cikin wata wasiƙar murabus da ya aika wa shugaban jam’iyyar na Gunduma ta Ɗaya da ke Aiyetoro Gbede, ƙaramar hukumar Ijumu a Jihar Kogi, wacce ke ɗauke da kwanan wata 4 ga Yuli, 2025, Melaye ya bayyana rashin tsari da inganci a cikin jam’iyyar a matsayin manyan dalilan ficewarsa.
Ya nuna ɓacin ransa kan yadda ya ce PDP ta gaza samar da hanyoyi masu ma’ana wajen magance manyan matsalolin siyasa da ke damun ƙasa, waɗanda ya bayyana a matsayin “ƙuraje” da ke hana cigaban Najeriya.
Melaye ya bayyana cewa yanayin da ake ciki a halin yanzu ya sanya ya zama dole a gare shi ya dakatar da duk wani mu’amala da jam’iyyar saboda dalilai na ɗabi’a da ƙwarewa. Saboda haka, ya sanar da janyewarsa daga dukkan harkokin jam’iyyar da kuma soke membobinsa daga PDP nan take.
