Hukumar Kula da Tsarin Fansho na Ma’aikatan Jiha da Kananan Hukumomi ta Jihar Jigawa ta raba sama da naira biliyan 1.5 ga tsofaffin ma’aikata 569 da suka yi ritaya.
Da yake jawabi ga masu amfana da kudin a harabar gidan Fansho kafin fara rabon, Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad K. Dagaceri, ya bayyana tsarin fansho na Jigawa a matsayin ɗaya daga cikin mafi nagarta a Najeriya.
Ya bayyana cewa fiye da jihohi ashirin ne suka kai ziyara Jigawa domin koyon yadda ake tafiyar da tsarin fansho cikin gaskiya da nagarta.
Alhaji Dagaceri ya yaba wa Gwamna Umar A. Namadi bisa jajircewarsa da goyon bayansa ga ci gaba da kuma ƙarfafa tsarin fansho tun bayan hawansa mulki.
Ya jaddada irin tasirin da irin wannan jajircewa ke yi wa rayuwar tsofaffin ma’aikata da ma’aikatan da ke kan aiki, yana mai rokon su da su ci gaba da addu’a ga gwamnati domin cimma manufofinta da kuma yaba wa kokarin da Gwamna Namadi ke yi.
A nasa jawabin, Babban Sakataren Hukumar Fansho, Dr Bilyaminu Shitu Aminu, ya sanar da cewa jimillar kuɗin da za a raba wa tsofaffin ma’aikatan ya kai Naira 1,505,449,327.78.
Ya bayyana cewa kuɗin sun haɗa da nau’o’in biya daban-daban kamar kudin ritaya, kudin mutuwa da kuma saura-sauran hakkokin da suka shafi fansho.
Dr Aminu ya ce daga cikin wadanda za a biya, 287 sun fito ne daga aikin gwamnati na jiha, 158 daga ma’aikatan kananan hukumomi, sannan 124 daga Ma’aikatar Ilimi ta Kananan Hukumomi (LEA).
Musamman, ya bayyana cewa:
Naira 875,625,045.00 za a biya tsofaffin ma’aikatan jihar,
Naira 355,025,795.72 ga tsofaffin ma’aikatan kananan hukumomi,
Naira 274,798,487.06 kuma za a raba wa tsofaffin ma’aikatan LEA.
Babban Sakataren ya sake jaddada kudirin hukumar na ci gaba da biyan duk wani haƙƙi na ma’aikata akan lokaci, ciki har da biyan fansho na wata-wata a mako na farko na kowane wata.
Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na ci gaba da mayar da hankali wajen inganta rayuwar ma’aikatanta, domin tabbatar da cewa suna jin daɗin rayuwa bayan kammala aikin yi.


