Trends

WAFCON: Super Falcon ta Lallasa Morocco da Ci 3 – 2

Ƙungiyar Super Falcons ta lashe kofin gasar Afrika na WAFCON karo na goma
Ƙungiyar kwallon kafar Najeriya ta mata wato Super Falcons ta lashe kofin gasar Afrika na WAFCON karo na goma tare da hana Morocco kofin tarihi na farko. Najeriya ta lallasa Morocco da ci 3 da 2 da za a iya cewa ƴan wasan Najeriya sun dau fansa kan Morocco da ta yi waje da su a wasan kusa da na karshe a shekarar 2022.

Super Falcons, wadda ta samu tagomashi sosai bayan ta doke Afrika ta Kudu mai rike da kofin gasar a wasan kusa da na karshe, ta lashe kofin karo na goma a gasar sau 13.

A gaban magoya bayan Morocco a gida, ‘yan wasan Atlas Lionesses sun yi rashin nasara a karo na biyu a jere, bayan da suka yi rashin nasara a wasan karshe a shekarar 2022, kuma a gida.

‘Ƴan Najeriyar sun ba wa kansu tsoro sosai inda suka zura kwallaye biyu a cikin mintuna 25 na farko.

Kyaftin din Morocco, Ghizlane Chebbak, ta fara cin kwallo bayan mintuna 13 da soma wasan da wata kyakkyawar bugun daga gefe.

Sanaâ Mssoudy ce ta zura kwallo ta biyu da bugun tazara bayan mituna24.

‘Yan wasan Najeriya da suka yi fice a zagaye na biyu, sun dawo ne a farkon rabin sa’a na karshe, inda da farko Esther Okoronkwo ta ci bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da Nouhaila Benzina ta saka hannu, wadda aka yi amfani da na’urar domin tabbatar da wannan kuskure.

Rahotanni daga hukumar ta CAF na cewa Morocco za ta karbi bakuncin wasan na gaba a 2026.