By Ibrahim Hamza Abuja
Manjo Janar Abdul Malik Jibrin, murabus ya ce lallai ilalla, za a jima kafim a lalubo dattijo da zai iya kwatsnta irin halayen dattako irin na marigayi tsohon shugaban kasa na mulkin soja da na farar hula iron marigayi Muhammadu Buhari.
Ya fadi haka ne yayin da ya kai bulaguro zuwa garin Daura domin yi wa iyalansa ta’aziyar rasuwan shugaban a soja da kuma siyasa.
Janam Jibrin wanda shine Sakataren Hukumar kula da Jami’an tsaron al’umma, da ta hukumar gyara halaye, da ta kashe gobara da kuma ta shige da fice, watau (CDCFIB).
Ya ce, “Janar Muhammadu Buhari, bawan Allah ne wanda zai dade kafin a sami wanda zai kwatanta irin hali da ayyukansa.
“Ina tuna lokacin da yake shugaban ‘Kasa, ya yi an gani, domin ba kasafai ake samun wanda ya rike mukamai daban-daban amma ba a kama shi da laifin ‘kuruciyar ‘Bera ba, idan aka yi la’akari da yadda wasu mutanen kasarnan suke da son azurta kansu da dukiyar jama’a.
“Amma wannan bawan Allah an gwada shi an gani tun kafin ya zama Shugaban Kasa, ya rike mu’kanin Gwamna, watau tun kafin a bashi mu’kamin gwamna, an san shi a matsayin mutum mai gaskiya.
“Akwai lokacin da aka tura shi aiki a kasar Indiya, da ya dawo, maimakon ya rike sauran chanji, sai ya mayarwa gwamnati.”
Janar Jibril ya ci gaba da cewa, Marigayin mutum ne mai tsoron Allah da gudun ta’ba kayan jama’a
Duk da mutum tara yake bai cika goma ba, dun ‘Dan Adam yana yana tabka kurakurai, amma idan aka dora a sikeli, za a ga ayyukan Buhari da yake yi wa jama’a na alkhairin sun fi kura-kuransa yawa.
Ya ‘kara da cewa, na godewa Allah da ya bashi tsawon rai da daman yi wa jama’a aiki kafin ya dauki kayansa. Ba inda aka taba furta cewa akwai wani da ya bashi wani na goro ko cin hanci domin ya yi algushshu. Duk wanda sika uo aiki da shi San haka. Za a dade kafin a Sami masu iron wannabe Hali.
Janar Jibrin ya jaddada cewa, Buhari mutum ne mai sadaukar da kai, don tarihi ya tabbatar da ya yi wa al’umma aiki, domin mu ganau ne, ba jiyau ba. Na zo Daura ne domin yi wa iyalansa da jama’a ta’aziya a matsayinsa na shugaba na a Soja da kuma a siyasa. Hausawa dai suna cewa: Ba rabo da gwani ba, kafin a mai da kamarsa. ‘Dan Adam baya rasa yin laifi, muna addu’ar Allah ya gafarta masa, amin.
