Kotun ta kori karar APC da ke neman hana kananan hukumomin Kano kudade Gwamnatin Tarayya

Birnin Kano

Wata babbar kotun tarayya da ke Kano ta yi watsi da karar da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta shigar, tana neman dakatar da rarraba kudaden gwamnatin tarayya ga kananan hukumomi 44 na jihar Kano da ke karkashin shugabancin jam’iyyar New Nigerian People’s Party (NNPP).

Karar, wadda aka shigar tun watan Nuwamba 2024, ta fito ne daga Shugaban APC na Kano, Prince Abdullahi Abbas, tare da Aminu Aliyu Tiga a matsayin wanda ake kara. Sun kalubalanci sahihancin zabukan shugabannin kananan hukumomin NNPP.

A cikin karar, an hada da wasu bangarori kamar su Babban Bankin Najeriya (CBN), Kwamitin Rarraba Kudaden Gwamnati (FAAC), Hukumar Kula da Rarraba Albarkatu da Tsare-tsaren Kudi (RMAFC), Akanta Janar na Tarayya, Ministan Kudi, Audita Janar na Tarayya, da kuma Attoni Janar na Tarayya.

Jam’iyyar APC ta nemi kotun ta bayyana cewa shugabannin kananan hukumomin ba su samu mukaman ne ta hanyar sahihin zabe ba, sabanin tanadin Sashe na 7(1) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999 (wanda aka gyara), don haka a haramta musu ci gaba da karbar kudaden gwamnatin tarayya.

APC ta kuma roki kotu da ta hana gwamnati, CBN, da Akanta Janar na Tarayya daga ci gaba da tura kudaden gwamnati zuwa ga kananan hukumomin.

Amma a hukuncin da ya yanke a ranar Litinin, mai shari’a Simon Amobeda ya ce kotu ta yi watsi da karar gaba daya, kuma ta ce ba za a iya dawo da ita ko sabunta ta ba a nan gaba.

Ko da yake mai shari’a Amobeda ya amince da bukatar wadanda ake kara na dakatar da shari’ar, ya jaddada cewa irin wannan bukata ya kamata a shigar da ita cikin kwanaki 14 bayan an mika musu karar, bisa tanadin Dokar Kotun, Order 50, Rules 3, 4 da 5.

Tun da farko, lauyan masu kara, Mr. Sunday Olowomoran, wanda ya wakilci babban lauya, Abdul Adamu-Fagge, SAN, ya bukaci kotun da baki da ta janye karar, inda ya ce, “Mai shari’a, an daukaka kara kan wannan shari’a, kuma kotun daukaka kara a ranar 30 ga Yuni ta bayyana cewa wannan kotu ba ta da hurumin sauraron wannan kara, cewa kotun jihar Kano ce kawai ke da ikon sauraren ta.”

Lauyoyin da suka wakilci CBN da RMAFC, Mr. B. D. Uche da S. G. Ahmad, sun bayyana cewa ba su cikin wadanda suka daukaka karar, kuma suka bukaci kotu da ta kori karar da hukuncin biyan N1 miliyan kowannensu.

Lauyan da ya wakilci Attoni Janar na Tarayya, Tajudeen Abdullahi, ya bukaci kotu da ta yi watsi da karar tare da hukuncin biyan N2.5 miliyan.

Lauyan gwamnatin jihar Kano, Bashir Yusuf-Muhammad, ya bukaci kotu da ta hukunta masu karar da tara har Naira biliyan 2 saboda bata lokaci da cin fuska ga doka.

Sani Mustafa-Dauda, wanda ya wakilci Attoni Janar na Kano, ya roki kotun da ta yi watsi da karar tare da tara ta N5 miliyan.

Lauyan hukumar KANSIEC, Ibrahim Wangida, ya roki kotu da kada ta soke karar kawai, sai dai ta kore ta baki daya. “Mai shari’a, hukumar KANSIEC ta sha wahala matuka – har ofishinmu ya kasance a rufe na tsawon watanni uku. Mun bi duk matakan shari’a. Don haka muna neman N2 miliyan,” in ji shi.

Lauya Eyitayo Fatogun, SAN, da ya wakilci kananan hukumomi 44, ya bukaci kotun da ta kori karar tare da hukuncin biyan N2 miliyan, bisa tanadin dokar kotun, Order 50.

Lauyan shugabannin kananan hukumomi 44, Mustapha Hussaini, ya roki kotun da ta kori karar tare da hukuncin biyan Naira miliyan 44.

A karshe, kotu ta kori karar kwata-kwata, lamarin da ke nuni da cewar jam’iyyar APC ta kasa cimma burinta na dakatar da kudaden gwamnatin tarayya zuwa kananan hukumomin da jam’iyyar NNPP ke jagoranta.