Makon Yan Jarida:  Sanata Al-Makura, Kakakin Majalisa Abbas, Arc. Dangiwa, Hilliard Eta Sun Samu Lambar Yabo

Mataimakin Shugaban NUJ na kasa, Momoh Adeiza, tsohon Shugaban NUJ Yankin D, Chris Isuguzo, Shugabar NUJ reshen FCT, Grace Ike, Sanata Umaru Tanko Al-Makura wanda ya karɓi lambar yabo ta NUJ FCT Personality of the Year 2025, da Shugaban NYSC, Hilliard Eta wanda aka karrama a matsayin Patron na NUJ FCT, a ranar Talata a birnin Abuja.

Daga: Ibrahim Hamza Abuja

Sanata Umaru Tanko Al-Makura, Shugaban Hukumar Ilimin Firamare ta Kasa (UBEC), ya samu lambar yabo tare da wasu manyan jiga-jigai saboda irin gudunmawar da suka bayar wajen cigaban kasa.

NUJ (Kungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya) reshen babban birnin tarayya (FCT) ta ba shi lambar yabo ta Media Personality Award 2025.

An mika masa lambar yabon ne ta hannun Mataimakin Shugaban NUJ na Yankin D (Zone D), Mista Momoh Adeiza, a wajen makon NUJ na shekarar 2025 da aka gudanar a Otal din Transcorp Hilton, Abuja, karkashin taken: “Jarida a Duniya Mai Sauyawa: ‘Yancin Fadin Albarkacin Baki, Kafofin Watsa Labarai, Dimokuradiyya da Al’umma.”

Sanata Al-Makura, wanda tsohon Gwamnan Jihar Nasarawa ne kuma shugaban taron, ya bayyana cewa, “A matsayina na tsohon gwamna, tsohon dan majalisa, kuma kafin haka, dan jarida, na shaida yadda kafafen yada labarai ke zama madubin al’umma da kuma lamirin zamantakewa. Jarida ba wai rahoton abubuwa ba ne kawai, ita ce jinin gaskiya da adalci, tushen dimokuradiyya da wakilin muradin jama’a.”

Ya kara da cewa: “Dimokuradiyya ba ta da wani amfani in har ba ta kare rayuka, haƙƙoƙi da walwalar jama’a ba. Ba za a iya cimma wannan ba tare da jaridu masu ‘yanci, wadanda za su iya tambaya, bincike da bayyanar da gaskiya, ko da kuwa tana da nauyi.”

Sanata Al-Makura ya gabatar da wasu shawarwari da suka hada da:

1. Tsarin Tsaro da Inshorar ‘Yan Jarida – musamman wadanda ke aiki a yankunan rikici da masu bincike.

2. Asusun Cigaban Jarida – da hadin gwiwar gwamnati da masu zaman kansu domin tallafa wa jaridu masu karamin karfi, da kuma horar da ma’aikata a fannin dijital.

3. Wayar da Kan Jama’a Game da Labarai – musamman a makarantu da unguwanni domin karfafa wa matasa gwiwa wajen fahimtar gaskiyar labarai da kauce wa shishshigi.

4. Kungiyar Kasa ta Binciken Gaskiyar Labarai – domin kawar da labaran karya musamman kafin zaben 2027.

A nasa bangaren, Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Abbas Tajudeen, a cikin jawabin sa mai taken “‘Yancin Jarida da Dimokuradiyya: Samar da Kwarewa ba tare da Rikici ba,” ya ce, “Kwanaki kadan da suka wuce, mun bude kofar Majalisar Wakilai ga al’umma ta hanyar shirin Open Week, inda kungiyoyi da jama’a suka samu damar tofa albarkacin bakinsu.”

Ya kuma bukaci kafafen yada labarai na Najeriya da su hada kai wajen bunkasa tsarin tantance gaskiyar labarai, ta hanyar hadin gwiwa tsakanin jaridu, kungiyoyin fararen hula, masu bincike na ‘yancin kai da hukumomin gwamnati.

Ministan Gidaje da Ci gaban Birane, Arc. Ahmed Musa Dangiwa, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya tana da shirin samar da gidaje masu saukin kudi ga ‘yan Najeriya, ciki har da Journalists’ Village a Abuja.

Shugaban Hukumar NYSC, Chief Ntufam Hilliard Eta, wanda aka nada a matsayin Patron na NUJ FCT Council, ya sha alwashin ci gaba da tallafawa kungiyar.

Taron ya samu halartar jiga-jigai da dama, ciki har da tsohon Shugaban Jami’ar Nasarawa State, Farfesa Mohammed Mainoma Akaro, Daraktan Cibiyar Al’adu ta kasar China, Mista Yan Jin Xi, da Mashawarci na Musamman ga Shugaban Kasa, Mista Sunday Dare.

A nata jawabin, Shugabar NUJ FCT Council, Comrade Grace Ike, ta bayyana cewa makon NUJ ba kawai biki ba ne, amma lokaci ne na yin nazari da kuma fuskantar ayyukan ci gaban kasa.