Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta sanya tsohon jirgin shugaban ƙasa kirar Boeing Business Jet (BBJ) wanda aka saya shekaru 20 da suka gabata a kasuwa don sayarwa a ƙasar Switzerland, bayan maye gurbinsa da sabon jirgi kirar Airbus A330.
Wannan jirgi na Boeing 737-700 BBJ, wanda aka saya a shekarar 2005 a lokacin mulkin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, yana cikin duba lafiyar injinsa a kamfanin AMAC Aerospace, da ke birnin Basel na Switzerland, kamar yadda aka bayyana a shafin Controller, wata babbar cibiyar tallace-tallacen jirage a duniya. Wannan jirgi ne ya kasance babban jirgin shugaban ƙasa a lokutan gwamnatoci da dama a Najeriya.
Shirin sayar da jirgin na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta kira da buƙatar rage kashe-kashen gwamnati da kuma ƙara bayyana gaskiya wajen tafiyar da kadarorin gwamnati, musamman na jiragen fadar shugaban ƙasa. Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ya kare sayen sabon jirgi Airbus ACJ330-200, yana mai cewa tsohon jirgin na Boeing ya yi tsufa kuma yana da tsada wajen gyara.
A cewarsa, “Tsohon jirgin BBJ ya daina yin aiki yadda ya kamata, kuma ya samu matsala a wani tafiya zuwa Saudi Arabia.” Onanuga ya kuma tabbatar da cewa an karɓi sabon jirgin Airbus a watan Yulin 2024 kuma yanzu shi ne ke matsayin jirgin shugaban ƙasa.
An gina jirgin Boeing a 2005, kuma ya yi kusan 3,821 na’urorin tashi da 1,881 saukowa. An shirya jirgin don ɗaukar fasinjoji 33 da ma’aikata 8 cikin wani tsari mai sassa biyar. Cikinsa ya ƙunshi ɗakin kwana na musamman da bandaki mai wanka, ofishin VIP, ɗakin taro da kujera irin na kasuwanci. Jirgin na dauke da Ka-band Wi-Fi, ADS-B Out, da FANS 1/A na’urorin zamani.
A watan Yulin 2024, an yi wasu gyare-gyare a cikin jirgin ciki har da canjin kafet da sabunta kujerun masu daraja. An kammala duba lafiyar injin (C1-C2 checks), sai dai ba a haɗa injin ɗin cikin shirin kulawar injin ba. Dukkan injinan, CFM56-7BE, suna aiki ne a matsayin “on condition,” wato ba su da tabbacin gyara a ƙarƙashin kowanne shiri na garanti. Ba a bayyana farashin da ake so a sayar da jirgin ba, ko dai daga AMAC Aerospace ko gwamnatin Najeriya.
Tun shekarar da ta gabata, an samu ce-ce-ku-ce game da sabon jirgin Airbus bayan rahotanni sun bayyana cewa gwamnati za ta kashe fiye da naira biliyan 150 wajen sayensa. Ƙungiyoyin farar hula da ‘yan ƙasa da dama sun nuna damuwa kan adadin kuɗin da kuma irin wahalhalun tattalin arziƙin da ƙasar ke fuskanta.
Sayar da jirgin Boeing ana kallon ta a matsayin yunkuri na gyara daidaito a cikin jiragen gwamnati tare da rage kashe kuɗi da ƙara lafiyar su. A halin yanzu, jirgin na nan yana kasuwa, amma ba a bayyana wanda zai saya ba.
