Trends

Wahalar Rayuwa: NLC ta Gargadi Gwamnati ta Gaggauta Inganta Rayuwa Yan Najeriya

Ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya NLC ta nemi gwamnati ta gaggauta magance talauci da al’ummar ƙasar ke fuskanta ta fuskoki da dama, kama daga hauhawar farashin abinci, tsadar lafiya, ababen hawa, matsalolin tsaro, rashin walwalar ma’aikata da dai sauransu.

Kiran na zuwa ne cikin bayanin bayan taro da ƙungiyar ta fitar ɗauke da sa hannun shugabanta Kwamred Joe Ajaero da sakatarenta Kwamred Emmauel Ugboaja, wanda aka kammala a Abeokuta da ke jihar Ogun a kudancin Najeriya.

Ƙungiyar ta bayyana damuwa matuƙa kan ta’azzarar matsin tattalin arziƙi, wanda ya jefa miliyoyin ‘yan Najeriya cikin talauci ta fuskoki da dama.

NLC ta ce lokaci ya yi da za’a kawo ƙarshen ɗaukar alƙawaruka, lokaci ne na ɗaukar mataki cikin gaggawa.

Ƙungiyar ƙwadagon ta yi barazanar ɗaukar mataki idan har gwamnati ta gaza kawo mafita game da talauci da matsalolin tsaro da al’ummar ƙasar suka tsinci kansu ciki.

Haka zalika, NLC ta buƙaci gwamnati ta ayyana dokar ta ɓaci kan matsalar tsaro tare da umartar rundunoninsu su sanya ƙafar wanda ɗaya da masu aikata laifuka, musamman ‘yan ta’adda.