Trends

Matatar Dangote ta Dakatar da Karɓar Naira, ta Fara Siyar da Fetur da Dala

Matatar Dangote ta fara amfani da dala wajen sayar da man fetur da sauran kayayyakin man fetur, inda ta kayyade farashin fetur daga matatar (ex-depot price) zuwa dala 0.779 kan kowace lita, tare da sanar da sabbin farashin dizal da man jiragen sama.

Wannan mataki na nufin kawo ƙarshen tsarin biyan kuɗin kayayyakin matatar da naira, wanda aka fara aiwatarwa a ƙarƙashin shirin naira-for-crude tun a watan Oktoban 2024.

Matatar ta bayyana cewa duk wasu takardun saye da aka fitar da naira da kuma yarjejeniyoyin da aka yi a baya da naira ba za su ƙara aiki ba.

A ƙarƙashin sabon tsarin farashi, an kayyade farashin dizal zuwa dala 1.087 kan kowace lita, man jiragen sama zuwa dala 0.942 kan kowace lita, yayin da aka sanya farashin jigilar fetur ta ruwa zuwa dala 1,044.62 kan kowace metric tonne. Sai dai cinikin iskar gas ta girki (LPG) bai sauya ba.

Jami’an matatar sun bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin daidaita kuɗin da ake sayar da kayayyakin matatar da kuɗin da ake sayen mafi yawan ɗanyen man da ake tacewa, wanda yanzu ake samu daga Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ta hanyar yarjejeniyoyin da ake biya da dala.

Wata majiya ta ce rashin daidaito tsakanin kuɗin sayen ɗanyen mai da kuɗin sayar da kayayyakin matatar, haɗe da sauye-sauyen farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya da kuma rashin tabbas kan canjin kuɗaɗen waje, ne suka sa aka koma amfani da dala.

Ana sa ran wannan mataki zai sauya yadda ake ƙayyade farashin man fetur a kasuwar mai ta Najeriya, inda Matatar Dangote ta zama mafi girman mai samar da tataccen mai a ƙasar.

‘Yan kasuwar da ke sayen fetur kai tsaye daga matatar za su riƙa la’akari da farashin musayar naira da dala, kuɗin sufuri da sauran kuɗaɗen da hukumomi suka tanada wajen ƙayyade farashin sayarwa ga masu amfani.

An ƙirƙiri tsarin naira-for-crude ne domin rage matsin buƙatar dala da kuma taimakawa wajen daidaita farashin man fetur, amma matsalolin aiwatar da tsarin sun sa an koma cinikin ɗanyen mai da dala.

Masana a fannin sun ce wannan sauyi ya sake nuna irin matsin da ake fuskanta a kasuwar canjin kuɗaɗen waje a Najeriya, tare da haifar da tambayoyi kan makomar shirin naira-for-crude da kuma tasirinsa ga farashin man fetur a cikin gida.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *