Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya haura dala 80 kan kowace ganga a ranar Litinin, bayan sabuwar takaddama tsakanin Amurka da Iran ta ƙara tayar da fargabar samun cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigin Strait of Hormuz, wata muhimmiyar hanyar jigilar mai a duniya.
Lamarin ya biyo bayan sanarwar Shugaban Amurka, Donald Trump, ta sanya harajin kashi 20 cikin ɗari kan kayayyakin da ke ratsa mashigin, tare da sake kafa takunkumin hana zirga-zirgar ruwa zuwa Iran. Wannan mataki ya haifar da girgiza a kasuwannin makamashi.
Rahoton OilPrice.com ya ce farashin danyen man Brent ya tashi daga kusan dala 76 zuwa sama da dala 80, bayan sabbin hare-haren makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa tsakanin ƙasashen biyu.
A wani saƙo da ya wallafa a dandalin Truth Social, Trump ya ce mashigin Hormuz zai ci gaba da kasancewa a buɗe, tare da jaddada cewa Amurka ta sake kafa takunkumin ruwan Iran.
Haka kuma, a wata hira da ya yi da Fox News, Trump ya ce Amurka za ta ci gaba da kula da mashigin, yana mai cewa ya kamata a biya ta saboda wannan aiki.
Sai dai Iran ta yi watsi da wannan shiri. Ministan Harkokin Wajen ƙasar, Abbas Araqchi, ya bayyana cewa Iran ce mai kula da mashigin tun da dadewa kuma za ta ci gaba da yin hakan, yana mai cewa sabon harajin da Amurka ta ƙaƙaba ya wuce kima.
Rundunar Revolutionary Guards ta Iran ta kuma yi gargaɗin cewa duk wani ƙarin tsoma bakin sojojin Amurka zai iya ƙara dagula harkokin mai da iskar gas a duniya.
A nata ɓangaren, Cibiyar Joint Maritime Information Centre ƙarƙashin jagorancin Rundunar Ruwa ta Amurka ta sanar da cewa za a fara aiwatar da takunkumin daga ranar Talata, wanda zai shafi dukkan tashoshin jiragen ruwa da matatun man Iran.
Sai dai cibiyar ta ce jiragen ruwa da ke wucewa zuwa wasu ƙasashe ba za a hana su ba, amma waɗanda suka ƙi bin sabon tsarin na iya fuskantar kama ko tsarewa.
A halin da ake ciki, Rundunar Tsakiyar Amurka (CENTCOM) ta ce ta kai hare-hare kan wani jirgin ruwa ƙarƙashin teku da wani wurin gyaran jiragen ruwa na Iran. Ita kuwa Iran ta ce ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka da ke Jordan, Bahrain da Kuwait.
Bayanan sa ido kan zirga-zirgar jiragen ruwa sun nuna cewa an fara takaita zirga-zirga ta mashigin Hormuz.
Sabuwar takaddamar ta jefa ayar tambaya kan yarjejeniyar wucin gadi da aka cimma a watan da ya gabata ta dakatar da rikici na tsawon kwanaki 60.
Masana sun bayyana cewa kusan kashi 20 cikin ɗari na yawan man da duniya ke amfani da shi a kullum na bi ta mashigin Hormuz, lamarin da ke nuna cewa duk wani cikas a yankin na iya yin tasiri sosai ga kasuwannin makamashi na duniya.
Haka kuma, wasu masana shari’a sun nuna shakku kan halaccin sabon harajin da Trump ya sanar, suna mai nuni da Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya kan Dokokin Teku, wadda ta tanadi ‘yancin zirga-zirga ba tare da tangarda ba a mashigai na ƙasa da ƙasa.
