Kasuwar hannayen jari ta Najeriya (NGX) ta samu gagarumar farfaɗowa a ranar Litinin, 8 ga Yuni, 2026, inda masu zuba jari suka sake sayen hannayen jari da yawa, lamarin da ya ƙara darajar kasuwar da Naira biliyan 514.97, tare da ɗaga jimillar darajar kasuwar zuwa Naira tiriliyan 156.11.
Alamar kasuwar gaba ɗaya ta All-Share Index (ASI) ta tashi da kashi 0.33 cikin ɗari zuwa maki 243,396.25, wanda ya ƙarfafa ribar da kasuwar ta samu tun farkon shekarar nan zuwa kashi 56.41 cikin ɗari, duk da sauye-sauyen da aka samu a baya-bayan nan da suka janyo asarar fiye da Naira tiriliyan 4.
Haka kuma, harkokin ciniki sun ƙaru sosai, inda aka yi musayar hannayen jari miliyan 746.18, wanda ya nuna ƙarin kashi 22.6 cikin ɗari. Darajar cinikin ta haura zuwa Naira biliyan 58.06, ƙarin kashi 81.3 cikin ɗari, yayin da yawan ma’amaloli ya kai 75,217, wanda ya nuna ƙarin kashi 36.2 cikin ɗari. Wannan na nuni da ƙarin shiga kasuwa daga manyan masu zuba jari da kuma ƙananan masu saka hannun jari.
Daga cikin kamfanonin da suka fi samun riba akwai International Energy Insurance da ta ƙaru da kashi 9.92 cikin ɗari, sai The Initiates Plc da kashi 9.91, ABC Transport da kashi 9.68, Abbey Mortgage Bank da kashi 9.63, da kuma UPDC REIT da kashi 8.91.
A ɓangaren masu asara kuwa, Fidson Healthcare ce ta fi faduwa da kashi 10 cikin ɗari, sai Academy Press da kashi 9.70, R.T. Briscoe da kashi 9.43, Sunu Assurances da kashi 9.38, da kuma Learn Africa da kashi 8.70.
Yawancin sassan kasuwar sun rufe da riba, inda sashen Mai da Iskar Gas ya ƙaru da kashi 0.87, Inshora da kashi 0.62, Bankuna da kashi 0.59, Kayayyakin Masarufi da kashi 0.37, da Kayayyakin Mabukaci da kashi 0.10. Sai dai sashen Kayayyakin Masana’antu ya yi ɗan koma baya da kashi 0.003.
Rahotanni sun nuna cewa manyan cinikai ne suka jagoranci yawan kuɗin da aka yi mu’amala da su, inda kamfanin Dangote Cement ya kaɗai ya samar da cinikin da ya kai Naira biliyan 29.77, fiye da rabin jimillar darajar cinikin ranar. A bangaren yawan hannayen jari da aka yi ciniki da su kuwa, FCMB Group ce ta fi kowanne kamfani, inda aka yi musayar hannayen jari miliyan 157.8, wanda ya kai kashi 21.15 cikin ɗari na dukkan ma’amalolin ranar.
Masana harkokin kasuwa sun bayyana cewa wannan farfaɗowar ta samo asali ne daga sabon sayen hannayen jari na kamfanoni masu ƙarfi kamar Oando, MTN Nigeria, Zenith Bank, GTCO da Aradel Holdings. Sun kuma bayyana cewa ana sa ran masu zuba jari za su ci gaba da nuna taka-tsantsan tare da sake daidaita fayilolin jarinsu a kwanaki masu zuwa.
