Trends

IATA Ta Rage Hasashen Ribar Kamfanonin Jiragen Zuwa Biliyan $100

Ƙungiyar Sufurin Jiragen Sama ta Duniya (IATA) ta rage hasashen ribar da kamfanonin jiragen sama na Afirka za su samu a shekarar 2026 zuwa dala miliyan 100, daga dala miliyan 200 da ta yi hasashe a watan Disambar 2025.

Sabon rahoton ya nuna cewa ribar za ta ragu daga dala miliyan 300 da aka samu a shekarar 2025, yayin da ribar kasuwanci za ta sauka zuwa kashi 0.2 cikin ɗari a 2026, idan aka kwatanta da kashi 1.6 cikin ɗari a shekarar da ta gabata. Haka kuma, ana sa ran ribar da ake samu daga kowane fasinja za ta faɗi zuwa dala 0.40 daga dala 2.10.

Duk da haka, IATA ta yi hasashen cewa buƙatar zirga-zirgar fasinjoji za ta ƙaru da kashi 10 cikin ɗari a shekarar 2026, wanda ya fi kashi 9.8 cikin ɗari da aka samu a 2025. Wannan na nuna yadda yawan matafiya ke ƙaruwa amma ribar kamfanonin ke ci gaba da raguwa.

Rahoton ya kuma nuna cewa ƙarfin ayyukan kamfanonin jiragen sama ba ya tafiya daidai da yawan buƙata. Ana sa ran kamfanonin za su ƙara yawan kujeru da jirage da kashi 7.7 cikin ɗari a 2026, ƙasa da kashi 8.7 cikin ɗari da aka samu a 2025.

A matakin duniya, IATA ta yi hasashen cewa kuɗaɗen shiga na masana’antar jiragen sama za su kai dala tiriliyan 1.165 a shekarar 2026. Sai dai ribar da za a samu gaba ɗaya za ta ragu zuwa dala biliyan 23, yayin da ribar kasuwanci za ta sauka zuwa kashi 2 cikin ɗari. Ana sa ran yankin Gabas ta Tsakiya zai fuskanci asarar dala biliyan 4.3, yayin da Turai da Arewacin Amurka za su ci gaba da samun riba, amma a matakin da ya ragu.

Kamfanonin jiragen sama na Afirka na ci gaba da fuskantar matsin lamba sakamakon tashin farashin man jiragen sama, raunin kuɗaɗen ƙasashe, ƙarancin ingantattun kayayyakin more rayuwa da kuma wahalar samun kuɗaɗen jari.

IATA ta bayyana cewa kamfanonin jiragen sama na Najeriya na cikin waɗanda suka fi fuskantar haɗari saboda ƙarancin amfani da hanyoyin kariya daga sauyin farashin mai da kuma matsalolin samun musayar kuɗaɗen ƙasashen waje.

Rahoton ya kuma yi nuni da rawar da Dangote Refinery ke takawa, bayan da matatar ta zama mafi girman mai fitar da man jiragen sama a duniya a watan Afrilun 2026, lamarin da ke sauya tsarin samar da man jiragen sama a duniya yayin da ake fuskantar matsalolin makamashi.

A ƙoƙarin rage tasirin tsadar man jiragen sama, gwamnatin Najeriya ta ƙaddamar da rangwamen kashi 30 cikin ɗari kan wasu kuɗaɗen haraji da caji da ake ɗorawa kamfanonin jiragen sama. Haka kuma ta kayyade farashin man Jet A1 a Legas tsakanin Naira 1,760 zuwa Naira 1,988 kan kowace lita.

Duk da waɗannan matakai, kamfanonin jiragen sama na ci gaba da rage wasu hanyoyin zirga-zirga tare da ƙara kuɗin tikiti domin shawo kan ƙalubalen da suke fuskanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *