Jamilu Gwamna ya Lashe Tikitin Takarar Gwamnan APC a Gombe.

Dr. Jamilu Ishiaku Gwamna ya lashe tikitin takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar APC bayan kammala zaben fidda gwani da aka gudanar a fadin jihar.

Tun da farko dai an zabi Dr. Gwamna a matsayin ɗan takarar maslaha na jam’iyyar APC daga hannun masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a wani taro da Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya kira.

Da yake sanar da sakamakon zaben, shugaban Kwamitin Gudanar da Zaben Fidda Gwanin Gwamna na APC, Sani Abubakar Danladi, ya ce an gudanar da zaben ne bisa tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2022 da kuma ka’idojin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, Independent National Electoral Commission, da kuma na jam’iyyar All Progressives Congress.

Ya bayyana cewa jimillar masu kada kuri’a 556,081 da aka tantance ne suka halarci zaben, wanda aka gudanar a dukkan kananan hukumomi 11 na jihar.

Dr. Jamilu Ishiaku Gwamna ya samu nasara a zaben bayan da ya samu kuri’u 247,161, inda ya doke sauran ‘yan takara biyu da suka fafata a zaben.

Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya samu kuri’u 12,120 inda ya zo na biyu, yayin da tsohon Ministan Sufuri, Saidu Ahmed Alkali, ya samu kuri’u 11,612 inda ya zo na uku.

Sanata Danladi ya kuma bayyana cewa kwamitin ya karɓi takardun janye takara daga hannun Farfesa Pantami da Sanata Alkali.

Sai dai ya ce an gabatar da takardun janar ne bayan fara aikin zaben, lamarin da ya sa sunayensu suka riga suka bayyana a takardun kada kuri’a, kuma har yanzu an ƙirga kuri’un da aka kaɗa musu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *