Hajjin 2026: Saudiya taGargaɗi Alhazai Kan Tsananin Zafi

Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa a Saudi Arabia ta gargadi alhazan da za su gudanar da aikin Hajjin shekarar 2026 da su shirya fuskantar matsanancin zafi, inda ake sa ran yanayin zafin zai kai har digiri 47 na ma’aunin Celsius a lokacin aikin Hajji.

Hukumar ta bukaci alhazan da su dauki matakan kariya domin gujewa kamuwa da cututtukan da ke da alaka da tsananin zafi, musamman yayin gudanar da ibadu a wajen harami a Makkah da sauran wuraren ibada masu tsarki da ke kewaye.

A cewar sanarwar, an shawarci alhazan da su rika daukar lema yayin zirga-zirga daga wuri zuwa wuri, tare da shan ruwa akai-akai domin kaucewa rashin ruwa a jiki.

Hukumomin sun kuma bukaci mahajjata da su guji daukar lokaci mai tsawo a karkashin hasken rana kai tsaye musamman a lokutan rana masu tsananin zafi, tare da bin umarnin lafiya da tsaro da jami’an Saudiyya za su bayar a duk tsawon aikin Hajjin.

Haka kuma an fitar da lambar gaggawa ta lafiya ta Saudiyya mai lamba 997 domin taimaka wa alhazan da ke bukatar agajin gaggawa na lafiya.

Wannan gargadi na zuwa ne yayin da miliyoyin alhazai daga sassa daban-daban na duniya ke ci gaba da isa Masarautar Saudi Arabia domin gudanar da aikin Hajjin bana.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *