Trends

WHO Ta Ayyana Dokar Gaggawa ta Duniya Kan Barkewar Ebola a Kongo da Uganda

Hukumar Lafiya ta Duniya (World Health Organization) ta ayyana barkewar cutar Ebola da ke faruwa a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) da Uganda a matsayin matsalar lafiyar jama’a ta gaggawa da ke shafar kasa da kasa, bayan an samu fiye da mutane 300 da ake zargi da cutar tare da mutuwar mutane 88.

Babban Daraktan WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya ce wannan barkewa ba ta kai matsayin annoba irin ta Covid-19 ba, don haka ya shawarci kasashe da kada su rufe iyakokinsu.

An bayyana cewa wani sabon mai dauke da cutar da aka tabbatar a Kinshasa, babban birnin Kongo, wanda ke da tazarar kusan kilomita 1,000 daga yankin da cutar ta fi tsananta a lardin Ituri, ya kara haifar da fargabar yaduwar cutar zuwa wasu wurare.

Haka kuma an samu rahoton masu cutar a lardin North Kivu, daya daga cikin yankuna mafi yawan jama’a a Kongo.

Hukumomin lafiya sun tabbatar cewa wannan barkewar cutar na da nasaba da nau’in kwayar cutar Ebola mai suna Bundibugyo, wadda ba kasafai ake samun ta ba kuma ba ta da rigakafi ko magani da aka amince da shi a hukumance.

An bayyana cewa wannan shi ne karo na uku da aka taba samun wannan nau’in cuta, bayan barkewar ta a Uganda tsakanin 2007–2008 da kuma a Kongo a 2012.

Shugaban Hukumar Kula da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC), Jean Kaseya, ya ce rikice-rikicen da ake fama da su, musamman tashin hankali, hijirar ma’aikatan hakar ma’adinai da rashin tsaro na kara dagula kokarin shawo kan cutar.

Ya ce, “Wannan barkewa ta fara ne a watan Afrilu, har yanzu ba mu gano tushen farko na cutar ba. Wannan na nufin ba mu san girman yaduwar cutar ba.”

WHO ta kuma bayyana cewa akalla ma’aikatan lafiya hudu sun mutu, yayin da yawan wadanda ke fitowa da sakamakon gwaji mai inganci, yaduwar zuwa Kampala da kuma yawaitar mutuwa a Ituri ke nuna yiwuwar cutar ta fi yadda ake gani a yanzu.

Sanarwar dokar gaggawa da WHO ta yi na da nufin jawo hankalin kasashe da kungiyoyin bayar da agaji domin tallafawa kokarin dakile yaduwar cutar, duk da cewa irin irin wadannan sanarwa a baya, kamar ta mpox a 2024, sun samu martani daban-daban daga kasashen duniya.

Hukumomi sun jaddada cewa akwai bukatar gaggauta hadin kai, sa ido kan yaduwar cutar da kuma samar da kayan aiki domin hana ta rikidewa zuwa babbar matsalar lafiya a yankin Afirka baki daya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *