Hukumar Kula da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (Nigeria Centre for Disease Control and Prevention) ta fitar da sanarwar gaggawa ga jama’a biyo bayan barkewar cutar Ebola a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) da kuma Uganda, tana mai tabbatar da cewa har yanzu ba a samu wani tabbataccen kaso na cutar a Najeriya ba.
A cikin sanarwar, hukumar ta ce tana ci gaba da gudanar da tsauraran matakan sa ido kan Ebola da sauran cututtuka masu yaduwa domin tabbatar da gano duk wani lamari cikin gaggawa da kuma daukar matakin dakile yaduwa idan ya taso.
Wannan gargadi ya biyo bayan karuwar damuwa a yankin, bayan hukumomin lafiya sun tabbatar da wasu sabbin masu dauke da cutar da ke da alaka da barkewar a yankin Afirka ta Tsakiya da Gabashin Afirka.
Nigeria Centre for Disease Control and Prevention ta bukaci ‘yan Najeriya da su kwantar da hankali tare da gujewa yada jita-jita ko labaran karya, tana mai jaddada muhimmancin dogaro da sahihan bayanai daga hukumomin lafiya.
Hukumar ta kuma shawarci jama’a da su rika wanke hannu akai-akai, gujewa cudanya da ruwan jikin masu rashin lafiya, tare da nisantar taba dabbobin da suka mutu ko cin naman namun daji da ba a tabbatar da asalinsu ba.
Haka kuma ta bukaci jama’a da su rika kai rahoton duk wani rashin lafiya da ba a saba gani ba zuwa asibiti mafi kusa, tana mai cewa gaggawar rahoto na da matukar muhimmanci wajen hana yaduwar cutar.
Nigeria Centre for Disease Control and Prevention ta tabbatar da aniyarta na kare lafiyar jama’a, inda ta ce za ta ci gaba da sa ido kan halin da ake ciki tare da fitar da sabbin bayanai a duk lokacin da bukata ta taso.
Domin karin bayani, hukumar ta ce jama’a za su iya kiran layin kyauta na 6232 ko ziyartar shafin ta na yanar gizo domin samun shawarwari da sabbin bayanai.
