Rahotanni sun nuna cewa ‘yan Najeriya sun kashe akalla tiriliyan ₦5.43 wajen sayen man fetur (PMS) a watanni ukun farko na shekarar 2026.
Binciken da aka yi kan alkaluman Hukumar Kula da Masana’antar Man Fetur ta Najeriya (NMDPRA) da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ya nuna cewa an amfani da lita biliyan 4.88 na fetur tsakanin watan Janairu da Maris, wanda matatar Dangote da kuma shigo da mai daga kasashen waje suka samar.
A watan Janairu kadai, an amfani da lita biliyan 1.87 na fetur da kudinsu ya kai tiriliyan ₦1.93, inda matsakaicin farashin kowace lita ya kasance ₦1,034.76.
A watan Fabrairu, amfani da fetur ya ragu zuwa lita biliyan 1.59, yayin da kudin da aka kashe ya kai tiriliyan ₦1.67, tare da matsakaicin farashin ₦1,051.47 kan kowace lita.
Sai dai a watan Maris, duk da cewa amfani da fetur ya sake raguwa zuwa lita biliyan 1.42, kudin da aka kashe ya karu zuwa tiriliyan ₦1.82 saboda hauhawar matsakaicin farashin zuwa ₦1,288.54 kan kowace lita.
Rahoton ya danganta tashin farashin da yakin da ke tsakanin Amurka da Iran da kuma karin farashin danyen mai a kasuwannin duniya.
Idan aka kwatanta da watanni ukun karshen shekarar 2025, lokacin da aka kashe tiriliyan ₦5.60 kan lita biliyan 5.32 na fetur, alkaluman shekarar 2026 sun nuna raguwar kashe kudi da kaso 3.04 cikin 100 tare da raguwar yawan man da aka saya.
Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da sabon rikicin shari’a tsakanin Aliko Dangote da gwamnatin tarayya kan lasisin shigo da mai.
Matatar Dangote ta shigar da kara a gaban kotu kan Babban Lauyan Tarayya, tana neman a soke lasisin shigo da fetur da aka bai wa Nigerian National Petroleum Company Limited da sauran ‘yan kasuwa.
Dangote ya yi zargin cewa bai kamata a rika bai wa kamfanoni lasisin shigo da mai ba idan matatun cikin gida na iya wadatar da kasar da fetur.
Sai dai kungiyar masu ajiyar mai da dillalan man fetur ta Najeriya (DAPPMAN) ta kare bayar da lasisin, tana mai cewa su ne ginshikin tsarin samar da fetur a Najeriya.
Kungiyar ta ce, “Lasisi su ne ke tabbatar da dorewar samar da fetur a Najeriya, ba wai don cutar da wani kamfani daya ba.”
DAPPMAN ta yi gargadin cewa soke lasisin zai iya jefa bangaren kasuwancin man fetur cikin matsala, tana mai cewa mambobinta sun zuba biliyoyin naira wajen gina ma’ajiyar mai da hanyoyin sufuri.
Kungiyar ta kuma jaddada cewa bai kamata muradun kasuwanci na masu zaman kansu su mamaye ikon hukumomin da ke kula da harkokin mai ba.
Yayin da Aliko Dangote ke cewa matatarsa na da karfin samar da duk bukatar kasar, dillalan mai na dagewa cewa har yanzu ba a kai matakin wadatar da bukata gaba daya ba.
Sabon rikicin ya sake bayyana takun-saka tsakanin masu tace mai a gida da masu shigo da mai daga waje yayin da Najeriya ke ci gaba da tafiyar da tsarin cire tallafin mai da kuma fuskantar hauhawar farashin makamashi a duniya.
