Jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta bayyana cewa Najeriya na daf da cin gajiyar ƙarin kuɗaɗen shiga daga ƙasashen waje, bayan da farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya ya haura dala $105 kan kowace ganga, wanda ya fi nisan da aka ɗora a kasafin kuɗin 2026 na dala $64.85.
Masana sun yi gargaɗi cewa idan rikicin Gabas ta Tsakiya ya ƙara tsananta har ya shafi mashigar Strait of Hormuz, farashin mai na iya kaiwa dala $150 kan ganga, lamarin da zai kawo babbar riba ga ƙasashen masu fitar da mai kamar Najeriya.
Tashin farashin na da alaƙa da matsalolin siyasa tsakanin Amurka da Iran, takunkumin da aka kakabawa man Rasha, da kuma tangarɗar samar da mai a ƙasashen Kazakhstan da Amurka. Najeriya, wacce ke samun sama da kashi 80 cikin 100 na kuɗaɗen shigarta daga mai, na iya amfana sosai daga wannan yanayi.
Babban Bankin Najeriya, Central Bank of Nigeria (CBN), ƙarƙashin gwamna Olayemi Cardoso, ya bullo da gyare-gyare kamar haɗa kasuwar musayar kuɗaɗen waje da inganta sarrafa kuɗi, wanda ya taimaka wajen rage tazara tsakanin farashin hukuma da na kasuwar bayan fage.
Sabbin bayanai sun nuna cewa darajar naira ta ƙarfafa zuwa ₦1,396.99 kan dala ɗaya, karo na farko da ta sauko ƙasa da ₦1,400 cikin sama da shekara guda. Haka kuma, ajiyar kuɗaɗen waje ta ƙaru zuwa dala biliyan 48.44, tare da hasashen kaiwa dala biliyan 51 kafin ƙarshen shekara.
Cardoso ya ce asusun ma’amalolin waje na ƙasa ya ƙaru da kashi 85 zuwa dala biliyan 5.28 a zangon biyu na shekarar 2025, sakamakon samar da mai da ya kai tsakanin ganga miliyan 1.45 zuwa 1.52 a rana, da kuma ƙarin fitar da kayayyakin da ba na mai ba da kashi 18 cikin 100.
Haka kuma, kuɗaɗen da ‘yan Najeriya ke turo wa daga ƙasashen waje sun ƙaru da kashi 12 cikin 100, yayin da gyare-gyaren da suka shafi tallafin mai, haraji da ƙarfafa bankuna ke inganta tsarin kuɗaɗen gwamnati.
Ya jaddada cewa: “Ba za a koma tsarin da Babban Banki ke ɗaukar nauyin gibin kasafin kuɗi ba.”
Masana sun ce haɗuwar ribar mai da gyare-gyaren tattalin arziki na ƙara ƙarfafa juriyar tattalin arzikin Najeriya, amma dorewar ci gaba zai dogara da ci gaba da aiwatar da tsare-tsare masu kyau, haɓaka yawan samar da kayayyaki da kuma ƙara amincewar masu zuba jari.







