Ƙungiyar ƙasashen masu samar da mai ta OPEC+ ta ƙara yawan ƙayyadadden mai da ake fitarwa da ganga 188,000 a rana domin watan Yuni, a wani mataki da masana ke cewa an ɗauka ne don nuna daidaito bayan ficewar ƙasar United Arab Emirates (UAE) daga ƙungiyar.
Ƙarin yawan samarwar ya samu amincewar ƙasashen Saudi Arabia, Russia, Algeria, Iraq, Kazakhstan, Kuwait da Oman, sai dai sanarwar hukuma ba ta ambaci UAE ba, wacce ta fice daga ƙungiyar kwanaki uku da suka gabata.
Wani masanin harkar makamashi, Jorge Leon na kamfanin Rystad Energy, ya ce yin shiru kan batun na nuna akwai takun-saka tsakanin mambobin ƙungiyar. Ya ce: “Ta hanyar ci gaba da bin tsarin samar da mai kamar yadda aka saba — amma ba tare da UAE ba — kamar suna nuna babu abin da ya faru, suna ƙoƙarin rage tasirin rikicin cikin gida tare da nuna cewa komai yana tafiya yadda ya kamata.”
Sai dai karin da aka yi wa ƙayyadadden samar da mai na iya rashin yin tasiri sosai, domin har yanzu fitar da mai daga ƙasashen yankin Gulf na fuskantar cikas sakamakon toshe mashigar Strait of Hormuz da Iran ta yi, wanda ke wuce kashi 20 cikin 100 na jigilar ɗanyen mai na duniya. Wannan ya biyo bayan hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila a watan Fabrairu.
Rahotanni sun nuna cewa samar da mai na OPEC+ ya riga ya gaza kai wa ƙayyadadden adadin da aka sa, inda a watan Maris aka samar da ganga miliyan 27.68 a rana, ƙasa da ƙayyadadden ganga miliyan 36.73, wato ragin kusan ganga miliyan 9, galibi saboda tasirin yaƙe-yaƙe.
Wata masaniya, Amena Bakr ta kamfanin Kpler, ta bayyana ficewar UAE a matsayin babban al’amari, tana mai nuna cewa ƙasar na da burin ƙara samar da mai zuwa ganga miliyan 5 a rana kafin shekarar 2027, sama da ƙayyadadden ganga miliyan 3.5 da aka ba ta a baya. Kamfanin mai na ƙasar, ADNOC, ya kuma yi alƙawarin zuba jarin dala biliyan 55 a sabbin ayyuka cikin shekaru biyu masu zuwa.
Ficewar UAE ta haifar da fargabar cewa wasu ƙasashe kamar Iraq da Kazakhstan na iya bin sahu, duba da zargin da ake musu na yawan karya ƙa’idar ƙayyadadden adadin samar da mai.
Duk da wannan rikici, OPEC+ ta jaddada cewa har yanzu ita ce ke da iko a kasuwar mai ta duniya, tana amfani da sauye-sauyen ƙayyadadden samar da mai a matsayin alamar ci gaba da daidaito, ko da yake a zahiri samar da mai na fuskantar ƙuntatawa.







