Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da sake tsawaita wa’adin sayarwa da kuma mika fom na tsayawa takara ga masu neman mukamai gabanin zaɓen 2027.
A cikin wata sanarwar manema labarai da aka fitar ranar Talata a Abuja, jam’iyyar ta ce sabon sauyin ya kuma shafi jadawalin tantance ‘yan takara, yayin da take ci gaba da daidaita tsare-tsarenta.
A cewar sanarwar da Sakataren Yaɗa Labarai na APC na ƙasa, Felix Morka, ya sanya wa hannu, sayar da fom na nuna sha’awa da na tsayawa takara zai ƙare da tsakar dare na ranar Laraba, 6 ga Mayu, 2026.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa an tsawaita lokacin mika cikakkun fom zuwa tsakar dare na ranar Alhamis, 7 ga Mayu, 2026.
Bisa sabon jadawalin, za a gudanar da tantance masu neman takara daga ranar Juma’a, 8 ga Mayu zuwa Talata, 12 ga Mayu, 2026, yayin da za a fitar da jerin sunayen waɗanda aka tantance a ranar Laraba, 13 ga Mayu, 2026.
APC ta bayyana cewa tsawaita wa’adin na da nufin bai wa masu neman takara ƙarin lokaci domin kammala dukkan matakan da ake buƙata, tare da tabbatar da gudanar da tsari cikin sauƙi gabanin zaɓen.







