Trends

2027: Zaben Bola Ahmed Tinubu na iya kawo karshen Najeriya — Hakeem Baba Ahmed

Shugaban jam’iyyar Peoples Redemption Party (PRP) na kasa, Hakeem Baba Ahmed, ya gargadi cewa sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu karo na biyu a 2027 na iya jefa Najeriya cikin matsananciyar barazana, idan halin da ake ciki a yanzu ya ci gaba.

A wata hira da ya yi da jaridar Nigerian Tribune, Baba Ahmed ya bayyana cewa kasar na fuskantar daya daga cikin mafi tsananin lokuta a tarihinta, inda rashin tsaro ya yawaita, talauci ke kara tsananta, kuma rarrabuwar kawuna tsakanin al’umma ke karuwa.

Ya zargi gwamnati da nesa da halin da talakawan Najeriya ke ciki, yana mai cewa mutane da dama sun rasa fata, musamman matasa da ba su da damar samun cigaba ko kwarin gwiwar gina makoma mai kyau.

A cewarsa, wannan yanayi ya haifar da rashin kwanciyar hankali, inda rashin amana da tashin hankali ke karuwa, kuma al’umma ke kara rarrabuwa ta fannoni daban-daban.

Ya jaddada bukatar sauyi mai muhimmanci a siyasa a shekarar 2027 domin dakatar da abin da ya kira hatsarin tabarbarewar da kasar ke ciki.

Ya ce: “Ba mu taba kasancewa cikin yanayin yaki kamar yadda muke ciki yanzu ba. Muna da gwamnati da ta yi nesa da jama’a. Ba su fahimci halin da ‘yan Najeriya ke ciki ba.

“Muna rayuwa ne a cikin mafi girman matsalar tsaro da muka taba fuskanta. Talauci ya kai matakin da ba a taba gani ba, matasa ba su da fata. Babu abin da zai karfafa musu gwiwa su zama ‘yan kasa nagari ko su tashi su gina makoma a kasa da ba ta kula da su ba.

“Muna fada da junanmu, muna kin juna. Kasar ta fi rarrabuwa yanzu fiye da kowane lokaci. Yana da matukar muhimmanci mu kawo karshen wannan halin a 2027. Kamar yadda na fada a baya, wani wa’adi na wannan gwamnati na iya kawo karshen kasar.”

Dangane da zargin cewa adawa da shugaban kasa na da alaka da wata hadakar siyasa, shugaban PRP ya karyata hakan, yana mai cewa barazanar da ake fuskanta ita ce karuwar aikata laifuka a fadin kasa.

Ya ce matsalar tsaro ta kara tsananta ne saboda gazawar gwamnati wajen dakile ayyukan ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata miyagun laifuka.

Baba Ahmed ya kara da cewa rashin jin dadin da ‘yan Najeriya ke nunawa ya samo asali ne daga wahalhalun rayuwa da suke fuskanta, ba wai wata hadakar siyasa ba.

Ya kara da cewa ya kamata a mayar da hankali wajen magance tushen matsalolin tsaro da kuma inganta rayuwar jama’a, maimakon jingina suka ga wata hadakar siyasa.

“Idan akwai wata hadaka, to hadakar masu laifi ne da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane, wadanda har yanzu shugaban kasa bai iya shawo kansu ba. Su ne kawai za su hada kai domin a ci gaba da kashe ‘yan Najeriya da talauta su.

“Ba wata hadaka ba ce. Shugaban kasa ya kasa tabbatar da tsaron ‘yan Najeriya, amma yana dora laifi kan ‘yan siyasa maimakon magance tushen matsalar tsaro.

“Idan ya ce akwai hadaka a kansa, ba daga wajen ‘yan kasa masu bin doka take ba, daga wadanda ke ganin ya kamata ya kare su ne. Wata kila akwai hadakar masu laifi da ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane—amma mu ba mu san da hakan ba.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *