Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da wani sabon kunshin tallafin jin daɗin ma’aikatan gwamnati, wanda ya haɗa da tsarin tallafin ritaya (Exit Benefit Scheme), tsarin diyya ga ma’aikata (Employee Compensation Scheme), da kuma shirin bashin gidaje na naira biliyan 10 ga ma’aikatan gwamnati.
Amincewar na daga cikin matakan da gwamnati ke ɗauka domin inganta walwalar ma’aikata, ƙara musu ƙwarin gwiwa da kuma haɓaka aiki a dukkan sassan gwamnati.
Daga cikin muhimman matakan da shugaban ƙasa ya amince da su akwai aiwatar da tsarin tallafin ritaya domin tallafa wa ma’aikata bayan sun kammala hidima, da kuma tsarin diyya da ke ba da kariya da tallafi ga ma’aikata yayin gudanar da aikinsu.
Haka kuma, Shugaba Tinubu ya amince da biyan cikakken kuɗin alawus na tafiyar aiki (Duty Tour Allowance) kashi 100 cikin 100 ga ma’aikatan da ke halartar shirye-shiryen horaswa, tare da sake dubawa da ƙara wasu alawus-alawus na musamman da ke da alaƙa da horo.
Ana sa ran sabbin matakan za su ƙarfafa haɓaka ƙwarewa, ƙara ƙaimin aiki da kuma inganta ingancin aiki a hukumomin gwamnati.
Bugu da ƙari, shugaban ƙasa ya amince da shirin bashin gidaje na naira biliyan 10 domin bai wa ma’aikatan gwamnati damar samun gidaje cikin sauƙi da kuma ƙara yawan masu mallakar gidaje.
Sabbin amince-amincen na nuna ƙudurin gwamnati na sake fasalta aikin gwamnati da kuma bai wa ma’aikata lada bisa gudummawar da suke bayarwa wajen gina ƙasa.
Masu lura da al’amura sun ce waɗannan tsare-tsare na iya inganta rayuwar ma’aikata matuƙa tare da ƙara amincewa da manufofin gyaran tattalin arzikin gwamnati.
