Hukumar Tattara Kuɗaɗen Shiga da Rarrabawa ta Ƙasa (RMAFC) ta fara wani shiri na tantance bayanai a duk faɗin Najeriya domin ƙarfafa tsarin raba kuɗaɗen shiga da tabbatar da adalci wajen rabon arziki tsakanin jihohi da ƙananan hukumomi.
Hukumar ta ce wannan aikin na da nufin duba abubuwan da ake amfani da su wajen raba kuɗaɗen shiga a ƙasa baki ɗaya, domin daidaita rabon da halin da ake ciki a yau na tattalin arziki da zamantakewa.
Da yake magana a wata hira da manema labarai, shugaban hukumar, Dakta Mohammed Bello Shehu, ya bayyana wannan mataki a matsayin wani babban ci gaba wajen ƙarfafa tsarin mulkin tattalin arziki na tarayya da kuma inganta shirin ci gaban ƙasa.
Ya ce sahihan bayanai da aka tantance su ne ginshiƙin tsarin raba kuɗaɗen shiga mai adalci da dorewa.
“Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa tsarin raba kuɗaɗen shiga a Najeriya ya dace da halin da ake ciki a zahiri. Ingantattun bayanai su ne tubalin adalci, daidaito da haɗin kan ƙasa. Wannan aiki na ƙasa baki ɗaya yana nuna ƙoƙarinmu na gina tsarin rarraba kuɗaɗe mai gaskiya da kuma mai amsa bukatun ‘yan ƙasa,” in ji shi.
Shehu ya yi kira ga gwamnatocin jihohi, ƙananan hukumomi, sarakunan gargajiya, ƙungiyoyin farar hula da shugabannin al’umma da su ba da cikakken haɗin kai ga ƙungiyoyin da ke gudanar da aikin tantancewar.
A cewarsa, sakamakon wannan aiki zai yi tasiri mai yawa ga tsare-tsaren ƙasa, sarrafa kuɗaɗe da kuma daidaiton ci gaban yankuna.
Ya ƙara da cewa aikin na daga cikin wajibin doka kuma wata muhimmiyar manufa ce ta ƙasa domin ƙarfafa amincewa da hukumomi da kuma tallafa wa tsara manufofi bisa hujjoji.
A cikin tsarin aiwatar da shirin, RMAFC ta bayyana cewa za a gudanar da aikin tantancewar ne daga yanki zuwa yanki a dukkan jihohi 36 da Babban Birnin Tarayya (FCT).
Hukumar ta ce aikin zai haɗa da tattara bayanai, tantance su da kuma daidaita muhimman bayanan zamantakewa da tattalin arziki da ake amfani da su wajen ƙididdige rabon kuɗaɗen shiga tsakanin jihohi.
Ta ƙara da cewa za a mai da hankali kan fannoni kamar ilimi da kiwon lafiya, ƙarfin samar da kudaden shiga na cikin gida, da kuma bunƙasar ababen more rayuwa a jihohi da ƙananan hukumomi.
Har ila yau, hukumar ta bayyana cewa za a gudanar da tarurrukan masu ruwa da tsaki a kowace jiha domin ƙara bayyana gaskiya, gina amincewa da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da al’umma.
Shehu ya ce tsarin raba kuɗaɗen shiga na ƙasa yana dogara ne kan ƙididdiga irin su yawan jama’a, girman ƙasa, ababen more rayuwa da kuma matakan ci gaban zamantakewa, waɗanda ke buƙatar sabuntawa lokaci zuwa lokaci domin dacewa da sauye-sauyen da ake samu.
“Tsawon lokaci, Najeriya ta samu manyan sauye-sauye a fannin zamantakewa da tattalin arziki, ciki har da ƙaruwa a yawan jama’a, faɗaɗa ababen more rayuwa, ƙaruwa a birane da kuma bambance-bambancen ci gaba tsakanin yankuna. Wadannan canje-canje na buƙatar sake tantance bayanai domin tabbatar da adalci da gaskiya wajen raba kuɗaɗe,” in ji shi.
Shugaban RMAFC ya kuma bayyana cewa duba tsarin raba kuɗaɗen shiga na ƙasa ya kai mataki mai nisa, inda wannan aikin tantance bayanai ke da matuƙar muhimmanci wajen tabbatar da inganci da sahihancin rabon kuɗaɗe a gaba.
Ya ƙara da cewa ƙungiyoyin hukumar za su yi aiki tare da ma’aikatu, hukumomi da cibiyoyin gwamnati, ƙananan hukumomi da kuma al’ummomi a duk faɗin ƙasa domin tabbatar da cewa dukkan bayanan da ake amfani da su sun dace da halin da ake ciki a yau.
