Shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya rubuta wa majalisar dattawa wasika yana neman amincewarta domin karɓo sabon rance na dala miliyan 516,333,070.
A cikin wasikar da aka aike wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, wadda aka karanta a zaman majalisar na ranar Alhamis, an bayyana cewa za a karɓo rancen ne daga Deutsche Bank.
Wasikar ta nuna cewa za a yi amfani da kudaden ne domin tallafa wa tsarin bashin da aka riga aka amince da shi a baya.
Shugaba Tinubu ya kuma roƙi majalisar da ta gaggauta amincewa da buƙatar.
Bayan karanta wasikar, Akpabio ya miƙa ta ga kwamitin kula da basussukan cikin gida da na ƙasashen waje domin duba ta tare da gabatar da rahoto cikin mako guda.



