Rikicin Shugabancin ADC: Kotun Koli Ta Ajiye Hukunci

Kotun Koli ta Najeriya a ranar Laraba ta ajiye hukunci kan rikicin shugabanci da ke addabar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Kwamitin alkalai biyar na kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Mohammed Garba, ya ɗage yanke hukunci bayan sauraron hujjoji daga ɓangarorin da ke cikin shari’ar.
Ƙarar mai lamba SC/CV/180/2026, tsohon shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, ne ya shigar.

Mai ƙarar, wanda ke jagorantar wani ɓangare na jam’iyyar da manyan ‘yan adawa ke goyon baya, yana neman a soke hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara na ranar 12 ga Maris, wanda ya ce ya saba da adalci.

Ya yi zargin cewa Kotun Ɗaukaka Ƙara ta wuce iyakokinta ta hanyar umartar a ci gaba da riƙe halin da ake ciki kafin rikicin (status quo ante bellum), a wata ƙara da wasu mambobin jam’iyya masu ƙorafi ƙarƙashin jagorancin Nafiu-Bala Gombe suka shigar.

Mark ya jaddada cewa rikicin ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyya ne, wanda kotuna ba su da hurumin tsoma baki a kai.

Baya ga Gombe, sauran waɗanda ake ƙara sun haɗa da jam’iyyar ADC, Sakataren Ƙasa Rauf Aregbesola, Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC), da tsohon Shugaban Ƙasa na jam’iyyar, Cif Ralph Nwosu.

Daga cikin buƙatun da Mark ya gabatar, akwai umarnin hana INEC amincewa da kowa a matsayin shugabancin jam’iyyar sai shi da sauran shugabannin da ke kan muƙami a halin yanzu, har sai an yanke hukunci kan ƙarar.

Haka kuma ya nemi a hana INEC sauya tsarin shugabancin jam’iyyar yadda yake a yanzu, tare da dakatar da ci gaba da shari’a mai lamba FHC/ABJ/CS/1819/2025 da ke gaban Mai shari’a Emeka Nwite a Kotun Tarayya da ke Abuja, har sai an kammala sauraron wannan ƙara.

Yayin da lauyoyin Mark ƙarƙashin jagorancin Jubril Okutepa, SAN, suka amince da takardun hujjojinsu, sun dage cewa wannan lamari na cikin gida na jam’iyya ne wanda ba abin shari’a ba ne, kamar yadda Kotun Koli ta taɓa yanke hukunci a baya.

Ko da yake INEC ba ta shigar da wata takarda don goyon baya ko ƙin amincewa da ƙarar ba, sauran ɓangarorin sun roƙi Kotun Koli da ta yi watsi da ƙarar saboda rashin cancanta.
Sun kuma ce kotun farko ta riga ta fahimci hujjojin shari’ar, wadda har yanzu tana gabanta.

A ranar 1 ga Afrilu, INEC ta cire sunayen Mark da Aregbesola daga shafinta na yanar gizo a matsayin Shugaban Ƙasa da Sakataren jam’iyyar ADC, bisa ga hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara.

Hukumar ta bayyana cewa, bisa umarnin ci gaba da riƙe halin da ake ciki kafin rikici, ba za ta amince da kowane ɓangare daga cikin masu rikicin ba har sai an warware batun a kotu.

Sai dai duk da wannan mataki na INEC—wanda ɓangaren Mark ya buƙaci Kotun Koli ta soke—jam’iyyar ADC ta jaddada cewa za ta ci gaba da shirye-shiryen gudanar da babban taronta na ƙasa kamar yadda aka tsara.

A ranar 14 ga Afrilu, Mai shari’a Emeka Nwite na Kotun Tarayya da ke Abuja ya ɗage sauraron ƙarar ta asali ba tare da sanya sabon lokaci ba (sine die), wadda Nafiu-Bala Gombe ya shigar domin tsige shugabancin jam’iyyar ƙarƙashin Mark.

Mai shari’ar ya ce ba zai iya ci gaba da shari’ar ba saboda akwai wani ɓangare na batun da ke gaban Kotun Koli.
Ya ƙara da cewa ci gaba da sauraron shari’ar zai zama “rashin bin ƙa’idar shari’a” yayin da ake jiran hukuncin Kotun Koli.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *