Gwamna Yusuf Ya Nemi Majalisa su Tantance Garo a Matsayin Mataimakin Gwamna

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya miƙa sunan Murtala Sule Garo ga Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da kuma amincewa da shi a matsayin Mataimakin Gwamna.

An bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ta ce matakin ya yi daidai da tanadin Sashe na 191(3) na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na shekarar 1999, wanda ya bai wa gwamna ikon naɗa mataimaki idan kujerar ta zama ba mai ita.

Kujerar Mataimakin Gwamna ta zama fanko ne bayan murabus ɗin Abdussalam Gwarzo a ranar 27 ga Maris, 2026.

Gwamnan ya bayyana cewa naɗin ya biyo bayan tattaunawa da shawarwari da manyan masu ruwa da tsaki a faɗin jihar, tare da roƙon Majalisar Dokoki da ta gaggauta duba buƙatar domin yanke hukunci.

Garo mai shekaru 48, an bayyana shi a matsayin gogaggen ɗan siyasa da mai gudanarwa, wanda ya shafe sama da shekaru ashirin yana aiki a fannoni daban-daban na mulki, na zaɓe da na naɗi.

Daga cikin muƙaman da ya riƙe akwai Sakataren Tsare-tsare na Jam’iyyarsa a jiha, Mai Bai Wa Gwamna Shawara na Musamman, da kuma Shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo.

Haka kuma ya taɓa zama Shugaban Ƙungiyar Shugabannin Ƙananan Hukumomi ta Najeriya (ALGON) a Kano, Kwamishinan Harkokin Ƙananan Hukumomi da Masarautu, sannan ya kasance abokin takarar Mataimakin Gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen shekarar 2023.

Sanarwar ta ƙara da cewa wannan naɗi wani ɓangare ne na ƙoƙarin gwamnatin Yusuf na ƙarfafa harkokin mulki da inganta ayyukan yi wa al’umma hidima a Jihar Kano.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *