Farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya fadi sosai a ranar Juma’a bayan an sake bude mashigar ruwan Hormuz ga zirga-zirgar jiragen ruwa na kasuwanci, lamarin da ya rage fargabar katsewar samar da mai na dogon lokaci.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya tabbatar da bude mashigar a wani sako da ya wallafa a dandalin Truth Social, yayin da Ministan Harkokin Wajen Iran, Abbas Araghchi, ya bayyana cewa hanyar ta “bude gaba daya” muddin yarjejeniyar tsagaita wuta tana aiki.
“Dangane da tsagaita wuta a Lebanon, an ayyana cewa dukkan jiragen ruwa na kasuwanci za su rika wucewa ta mashigar Hormuz ba tare da wata matsala ba,” in ji Araghchi a wani sako da ya wallafa a X.
Trump ya maraba da matakin, amma ya jaddada cewa takunkumin rundunar ruwan Amurka kan tashoshin jiragen ruwa na Iran zai ci gaba da aiki har sai an cimma cikakkiyar yarjejeniya.
Bude mashigar ya janyo saukar farashin mai nan take a kasuwanni. Farashin danyen mai ya sauka zuwa kusan dala $86 kan kowace ganga, raguwar kusan kashi 10%, yayin da ‘yan kasuwa suka rage hasashen hadarin siyasa da ya yi tasiri a farashin a makonnin baya.
Wannan saukar farashi ya biyo bayan hauhawar da aka gani a baya, inda farashin ya haura dala $100 kan kowace ganga, sakamakon fargabar karancin mai bayan rufe mashigar a karshen watan Fabrairu.
Ga ‘yan Najeriya, wannan ci gaba na kawo dan sauki. Farashin man fetur ya tashi daga kusan ₦760 kan kowace lita a farkon rikicin zuwa kimanin ₦1,300, abin da ya kara tsananta tsadar rayuwa.
Masana sun ce sake bude mashigar na iya taimakawa wajen daidaita samar da mai a duniya a gajeren lokaci, duk da cewa har yanzu akwai barazana, musamman ganin cewa yarjejeniyar tsagaita wutar za ta kare a ranar 21 ga Afrilu.
