Trends

Kabiru Marafa ya Fice Daga Jam’iyyar APC Zuwa ADC

Senata Kabiru Garba Marafa

Tsohon Sanata, Kabiru Marafa, ya fice daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa African Democratic Congress (ADC) a ranar Alhamis.

Marafa, wanda ya taba zama mai kula da kamfen ɗin Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima a Jihar Zamfara a zaɓen 2023, ya kuma taba rike mukamin kwamishina a jihar, kuma ana saninsa a matsayin babban mai goyon bayan Shugaba Tinubu a yankunan Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Yayin da yake sanar da sauya sheƙarsa, Marafa ya zargi Shugaba Tinubu da ƙoƙarin haifar da rikice-rikice a tsarin dimokuraɗiyyar Najeriya.

A cewarsa, matakin ficewa daga APC ya biyo bayan wani muhimmin taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a Jihar Kaduna, inda ya yi tattaunawa mai zurfi da abokan siyasarsa da magoya bayansa.

Mai taimaka masa a bangaren sabbin kafafen yaɗa labarai, Mansur Haruna, ya bayyana a cikin wata sanarwa cewa bayan nazari mai zurfi kan makomar tafiyar siyasa, Sanata Marafa ya yanke shawarar komawa ADC.

A yayin taron, Marafa ya zargi APC mai mulki da “manipuleshan” na siyasa, ciki har da zargin yunƙurin amfani da bayanan National Identification Number (NIN) domin rajistar siyasa ta ɓangare.

Ya kuma soki yadda gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ke ƙoƙarin haddasa rikici da rudani a cikin jam’iyyun adawa.
Sai dai ya jaddada cewa babu wani matsin lamba ko rikicin siyasa da zai hana shi shiga ADC, yana mai cewa matakin na nuna ƙudirin ‘yantar da al’umma daga abin da ya kira “ƙangin siyasa”.

A baya, Marafa ya nemi tikitin gwamna na APC a 2019 amma bai samu goyon bayan tsohon gwamnan jihar ba, Abdulaziz Yari. Wannan rikici ya haifar da rabuwar kai a jam’iyyar.

Har ila yau, ya kai ƙarar APC kotu kan zaɓen fidda gwani, inda har ta kai ga Supreme Court of Nigeria wadda ta yanke hukuncin cewa ba a gudanar da zaɓen yadda ya kamata ba, tare da bai wa Peoples Democratic Party (PDP) dukkan kujerun da APC ta lashe.

Daga baya, Marafa ya sulhunta da Yari a 2021, amma suka sake rabuwa bayan APC ta sake rasa jihar a zaɓen 2023.
Tun daga lokacin, ya ci gaba da samun sabani da Yari da kuma ministan harkokin tsaro na ƙasa, Bello Matawalle, kan iko da jagorancin APC a jihar Zamfara.