Trends

Bankuna Sun Tara Naira Tiriliyan 4.65 Yayin da CBN Ta Kammala Shirin Ƙara Jari

Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sanar da nasarar kammala shirin ƙara jarin bankuna, inda bankunan ƙasar suka tara jimillar naira tiriliyan 4.65 cikin watanni 24 domin ƙarfafa tsarin kuɗi da tallafa wa ci gaban tattalin arziki.

CBN ya bayyana cewa shirin, wanda aka ƙaddamar a watan Maris 2024, ya samu gagarumar halartar masu zuba jari na cikin gida da na ƙasashen waje, abin da ke nuna ci gaba da amincewa da fannin banki na Najeriya.

A cewar bankin, kashi 72.55 cikin 100 na jarin an samo shi ne daga cikin gida, yayin da kashi 27.45 cikin 100 ya fito daga masu zuba jari na ƙasashen waje, lamarin da ke nuna cewa Najeriya na ci gaba da jan hankalin kasuwannin kuɗi na duniya.

Da yake magana kan lamarin, gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya ce shirin ƙara jarin ya ƙarfafa tushen jarin bankuna sosai, tare da ba su damar jure girgizar tattalin arziki da kuma ƙara ba da rance ga muhimman fannoni na tattalin arziki.
Ya ƙara da cewa shirin ya ƙara ƙarfafa tsarin kuɗi da kuma inganta kwanciyar hankali gaba ɗaya.

CBN ta kuma bayyana cewa bankuna 33 sun cika sabbin ƙa’idojin mafi ƙarancin jari, yayin da wasu kaɗan ke ci gaba da bin matakan doka da ƙa’idoji a cikin tsarin da aka tanada.

Sai dai ta tabbatar da cewa duk bankuna na ci gaba da aiki yadda ya kamata, ba tare da tangarda ga ayyukan abokan hulɗa ba a duk tsawon lokacin shirin.

Hukumar ta ƙara da cewa shirin ya inganta matsayin isasshen jari (capital adequacy) a fannin banki, inda ya wuce ma’aunin duniya na Basel, tare da inganta ingancin kadarori da kuma bayyananniyar bayanan kuɗi.

Ta kuma lura cewa an aiwatar da shirin ne tare da rage sassaucin ƙa’idoji a hankali domin tabbatar da dorewar tsarin a dogon lokaci.

Domin ci gaba da waɗannan nasarori, CBN ta ce ta ƙarfafa tsarin sa ido bisa haɗari, inda take buƙatar bankuna su riƙa yin gwaje-gwajen juriya (stress testing) akai-akai tare da tanadar isasshen kariya daga haɗurran da ka iya tasowa.

A ƙarshe, bankin ya sake jaddada kudurinsa na tabbatar da tsayayyen tsarin kuɗi mai ƙarfi da gaskiya wanda zai iya tallafa wa burin tattalin arzikin Najeriya.