Farashin danyen mai ya sauka a ranar Laraba bayan rahotannin cewa Amurka na shirin ficewa daga Iran cikin gaggawa, tare da yiwuwar komawa kai hare-hare na lokaci-lokaci idan bukata ta taso.
Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai na Reuters cewa ana shirin janye sojoji daga Iran domin kawo karshen yakin da ya fara a ranar 28 ga Fabrairu.
A cewar Reuters, Trump da manyan jami’an gwamnatinsa sun bayar da lokuta daban-daban kan lokacin da za a kawo karshen yakin. Ya ce a ranar Talata ana iya kawo karshen hare-haren soji cikin makonni biyu zuwa uku, amma bai bayar da takamaiman lokaci ba a hirar da aka yi da shi.
Ya ce, “Ba zan iya fada muku daidai ba… amma za mu fita cikin gaggawa,” tare da kara da cewa bayan ficewa, Amurka za ta iya komawa domin kai hare-hare na lokaci-lokaci kan wuraren Iran idan bukata ta taso.
Bayan wannan rahoto, farashin danyen man Brent crude ya fadi daga kusan dala $115 a ranar Talata zuwa $101 a yammacin Laraba, yayin da West Texas Intermediate ya kai $99.32 a lokaci guda. Rahotanni sun nuna cewa farashin ya sauka ne sakamakon fatan cewa rikicin zai ragu cikin gaggawa.
Sai dai har yanzu farashin mai ya fi na karshen watan Fabrairu sama da kashi 40 cikin 100, lokacin da yakin ya fara.
Har yanzu ba a tabbatar da ko yankin zai koma yadda yake kafin rikicin ba, domin har yanzu akwai tashin hankali mai tsanani.
Rundunar Islamic Revolutionary Guard Corps (IRGC) ta yi barazanar kai hare-hare kan kamfanonin fasaha da masana’antu na Amurka guda 18 a Gabas ta Tsakiya, ciki har da Microsoft, Google, Intel, Tesla, IBM, Apple, da Boeing.
IRGC ta bayyana wadannan kamfanoni a matsayin “halattattun wuraren hari,” tana zargin su da taimakawa wajen tsara da bibiyar hare-haren sojin Amurka da Isra’ila.
A wani bangare, yayin da yakin ke ci gaba da kawo cikas ga zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Strait of Hormuz, kamfanin mai na gwamnatin Brazil, Petrobras, ya kara farashin man jiragen sama da kusan kashi 55 cikin 100 a ranar Laraba, kamar yadda bayanai daga shafin kamfanin suka nuna.
Petrobras, wanda shi ne babban kamfanin samar da mai a Brazil, na sabunta farashin man jiragen sama a farkon kowane wata bisa la’akari da farashin mai a duniya da kuma canjin darajar kuɗi.
