Kamfanonin jiragen sama na Najeriya na fuskantar yiwuwar karin kudin tikitin tafiya sakamakon tashin gwauron zabi na farashin man jirgin sama (Jet A1), wanda ya karu da fiye da kashi 100 bisa rikicin Gabas ta Tsakiya da ya dagula samar da danyen mai a duniya.
Kafin rikicin, ana sayar da Jet A1 a kan ₦900 zuwa ₦995 kan kowace lita, amma yanzu farashin ya tashi zuwa tsakanin ₦2,500 da ₦2,700 gwargwadon filin jirgin da aka kai shi, lamarin da ya sa man fetur ya zama babban abin da ke kara kudin aiki ga kamfanonin jiragen sama.
Masu gudanar da kamfanonin sun bayyana cewa farashin tikitin jirgi na iya ninkuwa idan wannan yanayi ya ci gaba. A da, man jirgin sama na daukar kusan kashi 30 zuwa 35 cikin 100 na kudin aiki, amma yanzu ya kai kusan kashi 45, wanda ya rage wa kamfanoni zabin da ya wuce kara kudin tikiti.
Mai magana da yawun kamfanin United Nigeria Airlines, Chibuike Uloka, ya bukaci Hukumar Kare Gasa da Kare Masu Amfani (FCCPC) da ta tattauna da kamfanonin jiragen sama kan dorewar farashi.
Ya bayyana cewa duk da farashin man ya haura ₦2,000 kan kowace lita, har yanzu kamfanoni da dama na ci gaba da sayar da tikiti a kusan ₦195,000, yanayin da ya ce ba zai dore ba.
Uloka ya gargadi cewa idan farashin man ya kai ₦3,000 kan kowace lita, wasu kamfanonin jiragen sama na iya durkushewa saboda matsin lamba, lamarin da zai rage yawan jirage tare da kara tashin kudin tikiti.
“Abin da muke nema yanzu ba riba ba ce, sai dai mu iya gudanar da aiki yadda ya kamata,” in ji shi.
Kwararre a harkar jiragen sama, Samuel Caulcrick, ya bayyana cewa kudin man jirgin sama yanzu ya zarce kudin gyara a matsayin mafi girman kashe kudi ga kamfanonin jirage.
“Idan wannan bangare ya tashi, lallai zai shafi farashin kowanne kujera. Ya kamata mu sa ran karin kashi 20 zuwa 25 cikin 100 a farashin tikiti nan da kwanaki masu zuwa,” in ji shi.
Rikicin ya kuma fito da kalubalen samar da mai a Najeriya, inda har ma Matatar Dangote ta tilasta shigo da danyen mai saboda karancin samarwa a cikin gida.
Farashin danyen mai na Brent ya haura dala $112 kan kowace ganga, wanda ya zarce kasafin kudin Najeriya na dala $65 zuwa $69.
Masana sun yi gargadin cewa idan farashin mai ya ci gaba da tashi, dole ne za a dora nauyin ga fasinjoji, wanda zai kara kudin sufuri da farashin kayayyaki a fadin kasa, tare da kara dagula halin da bangaren jiragen sama ke ciki a Najeriya.
