Watanni uku bayan da Gwamnatin Tarayya ta fitar da bond na ₦501 biliyan domin biyan tsofaffin basussukan wutar lantarki, kamfanonin samar da wuta (GenCos) sun bayyana cewa har yanzu ba su karɓi ko sisin kwabo ba.
An kirkiro wannan bond ne a karkashin shirin Shugaban Ƙasa na rage bashin bangaren wutar lantarki (Presidential Power Sector Debt Reduction Programme), wanda ke da nufin biyan kimanin ₦4 tiriliyan da ake bin GenCos na wutar da suka samar wa cibiyar sadarwar lantarki ta kasa cikin shekaru goma da suka gabata.
Bincike ya nuna cewa kamfanonin GenCos guda biyar sun rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu a watan Janairun 2026, amma har yanzu ba a fara fitar da kuɗin ba.
Kamfanonin sun hada da First Independent Power Limited, Geregu Power Plc, Ibom Power Company Limited, Mabon Limited, da Niger Delta Power Holding Company Limited.
Babbar Sakatariyar Kungiyar Kamfanonin Samar da Wuta, Joy Ogaji, ta tabbatar da jinkirin, inda ta ce: “GenCos guda biyar ne kawai suka sanya hannu. Zuwa yanzu… babu wani biya da aka yi.”
An aiwatar da fitar da bond din ne ta hannun NBET Finance Company Plc, kuma an saye shi gaba daya, inda ya ja hankalin asusun fansho, bankuna, da masu sarrafa kadarori. Jami’ai sun bayyana hakan a matsayin hujjar amincewar masu zuba jari ga gyaran da ake yi.
Sai dai jinkirin biyan kuɗin na haifar da damuwa kan rashin wadataccen kuɗi a bangaren wutar lantarki da ke cikin matsin lamba. GenCos sun ce rashin biyan kudaden ya raunana kasafin kudinsu, ya rage kula da kayan aiki, kuma ya hana sabbin zuba jari.
Mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkar makamashi, Olu Verheijen, ta bayyana bond din a matsayin “sabon farawa mai karfi” wanda ya hada warware basussuka da kuma wasu gyare-gyare masu fadi.
Jimillar kudin da za a biya kamfanonin GenCos guda biyar ya kai ₦827.16 biliyan, wanda za a biya a kashi hudu-hudu.
Masu ruwa da tsaki a bangaren sun yi gargadin cewa ci gaba da jinkiri zai iya kara tsananta matsalolin aiki, ciki har da hauhawar farashi, sauyin darajar kudin waje, da matsalolin samar da iskar gas, wanda ke nuna cewa har yanzu akwai manyan matsaloli a tsarin kasuwar wutar lantarki ta Najeriya.
