Eid-el-Fitr: Gwamnatin Tarayya ta Sanar da Alhamin, Jumma’a Ranar Hutu

Olubunmi Tunji-Ojo Ministan cikin gida

Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun Alhamis 19 ga Maris da Juma’a 20 ga Maris, 2026 a matsayin ranakun hutu domin bikin Eid al-Fitr, wanda ke nuna karshen watan azumin Ramadan.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya sanar da hakan a madadin Gwamnatin Tarayya.

A wata sanarwa da Sakatare na dindindin a ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a ranar Talata, ministan ya taya al’ummar Musulmi murnar kammala azumin Ramadan cikin nasara.

Tunji-Ojo ya bukaci Musulmi da su ci gaba da rike kyawawan dabi’u kamar soyayya, karamci, zaman lafiya, hakuri da kuma sadaukarwa, wadanda aka koyar a lokacin azumi.

Har ila yau, ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci na biki wajen yin addu’a domin dorewar zaman lafiya, hadin kai da ci gaban kasa.

Yayin da yake yi wa Musulmi fatan murnar Sallah cikin farin ciki, ministan ya bukaci jama’a da su yi bikin cikin natsuwa tare da taimakawa marasa galihu a cikin al’umma.

Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya na nan daram wajen tabbatar da hadin kan kasa da zaman lafiya tsakanin dukkan ‘yan Najeriya.