Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin ware kashi 5 cikin 100 na Jimillar Arzikin Cikin Gida (GDP) na Najeriya a kowace shekara domin tallafa wa harkokin bunkasa masana’antu, karkashin sabon Tsarin Ci gaban Masana’antu na Najeriya (Nigeria Industrial Plan) da aka kaddamar.
An bayyana tsarin a Abuja ta hannun Ma’aikatar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, inda aka ce manufar ita ce kara gudunmawar bangaren kere-kere zuwa kashi 15 cikin 100 na GDP nan da shekarar 2030, da kuma kashi 25 cikin 100 nan da 2035. Haka kuma ana sa ran bangaren hakar ma’adanai zai kai kashi 8 cikin 100 nan da 2030 da kuma kashi 10 cikin 100 nan da 2035.
Wani muhimmin ginshiki na shirin shi ne samar da isasshen kudade.
Gwamnati za ta kara jarin Bank of Industry zuwa Naira tiriliyan 3 nan da shekarar 2026, tare da fadada kudaden tallafi na musamman a Central Bank of Nigeria domin samar da rancen dogon lokaci ga bangarorin da aka bai wa fifiko.
Karamin Ministan Masana’antu, John Enoh, ya bayyana shirin a matsayin sauyi mai muhimmanci a manufofin kasa, inda ya ce an fifita bangarorin karafa, mai da iskar gas, gine-gine da kuma kere-kere a matsayin wuraren da za a fara mayar da hankali.
Shirin ya kuma bullo da sabon tsarin Economic Development Incentive, wanda zai maye gurbin tsohon tsarin Pioneer Status Incentive, inda za a rika bai wa kamfanoni rangwamen haraji bisa sakamakon da suka cimma kamar yawan zuba jari, karfin samarwa da samar da ayyukan yi. Haka kuma an kirkiro da tsarin dawo da wani bangare na kudin ruwa (Interest Drawback Scheme) ga kananan da matsakaitan masana’antu (MSMEs), idan sun cika sharuddan samar da ayyukan yi da kara fitar da kaya waje.
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya jaddada cewa hadin kai tsakanin bangarorin makamashi, kasuwanci, kayayyakin more rayuwa, kudi, horo da kirkire-kirkire shi ne zai tabbatar da nasarar shirin. Ya ce, “Yana bukatar tsari mai ma’ana da hadin gwiwa tsakanin gwamnati da bangare mai zaman kansa.”
Shirin ya kuma mayar da hankali kan dorewar muhalli, inda ake sa ran kashi 25 cikin 100 na makamashin da masana’antu za su rika amfani da shi ya kasance daga makamashi mai sabuntawa nan da shekarar 2030, daidai da manufar sauyin makamashi ta Najeriya da burin kai wa ga fitar da hayaki sifili nan da 2060. Haka kuma an jaddada fadada bincike da kirkire-kirkire (R&D), amfani da na’urorin zamani da sarrafa kansa a masana’antu.
Shirin, wanda aka tanadi taswirar aiki ta shekaru biyar (2025–2030), na da burin mayar da Najeriya cibiyar samar da kayayyaki a yankin Afirka karkashin yarjejeniyar AfCFTA, rage dogaro da kayayyakin waje, kara fitar da kaya, da kuma samar da ayyukan yi tare da rage talauci musamman a bangarorin sarrafa kayan gona, magunguna da sinadarai na mai.
