Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bayyana cewa yana iya shiga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hukumance, inda ya ce a halin yanzu yana cikin “tsaka-tsakin sauyin siyasa”.
Janar Musa ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi a shirin Sunday Politics na Channels Television, lokacin da aka tambaye shi ko yanzu yana kallon kansa a matsayin ɗan siyasa.
“Ban kammala sauyawa ba tukuna. Ina cikin sauyi,” in ji shi.
Da yake ƙarin bayani kan yiwuwar shiga jam’iyyar mai mulki, tsohon Shugaban Hafsoshin Tsaro (Chief of Defence Staff – CDS) ya amince da rawar da gwamnatin APC ta taka a tafiyar aikinsa na hidimar ƙasa.
“Ba tukuna ba, amma ina tsammanin zan shiga. Hakika. APC ta ba ni damar gabatar da kaina tun daga lokacin da nake CDS har zuwa yanzu, don haka me ya hana?” in ji Musa.
Ministan tsaron mai shekaru 58 ya kuma nuna cikakken goyon bayansa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya yi alkawarin biyayya da goyon baya ga gwamnatin, har da yiwuwar wa’adi na biyu.
“Shugaban ƙasa na buƙatar dukkan goyon baya. Zan ba shi cikakken goyon baya, duk abin da zan iya yi domin tabbatar da nasararsa a aikin da aka ɗora masa, har da ci gaba zuwa wa’adi na biyu. Zan ba shi duk abin da nake da shi,” in ji Musa.
Janar Musa ya yi aiki a matsayin CDS na 18 daga 23 ga Yuni, 2023, har zuwa ritayarsa a 30 ga Oktoba, 2025.
Daga bisani, Shugaba Tinubu ya rantsar da shi a matsayin Ministan Tsaro a ranar 4 ga Disamba, 2025.
Maganganunsa sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun sauyin sheƙa zuwa APC tun bayan hawar Shugaba Tinubu kan mulki a Mayu 2023. Wannan lamari ya ƙara ƙarfi musamman a cikin shekarar 2025 zuwa 2026, inda gwamnonin jihohi da dama masu ci suka fice daga jam’iyyun adawa zuwa jam’iyyar mai mulki.
Yayin da ake danganta yawancin sauyin sheƙar da rikice-rikicen cikin gida a jam’iyyun adawa, ƙara yawaitar sauye-sauyen siyasar ya ƙara zafafa muhawara kan yanayin siyasar Najeriya gabanin zaɓen gama-gari na 2027.
