Matatar Dangote Ta Ɗaga Farashin Mai Fetur Zuwa ₦799 Kan Lita

Matatar Mai ta Dangote ta ƙara farashin fetur (Premium Motor Spirit – PMS) daga ₦699 zuwa ₦799 kan kowace lita a farashin da ake fitarwa daga matatar (ex-gantry), lamarin da ya jawo tashin farashin famfo a gidajen mai na abokan hulɗarta, ciki har da kamfanin MRS Oil Nigeria Plc.

Sabon farashin, wanda ya fara aiki nan take, na nufin ƙarin ₦100 kan kowace lita. Wannan ƙarin ya zo ne bayan karewar tallafin wucin-gadi da matatar ta samar a lokacin bukukuwan ƙarshen shekara.

Bayan wannan sauyi, gidajen mai na MRS sun fara sayar da fetur kusan ₦839 kan kowace lita, wanda ya haɗa da kuɗaɗen sufuri, rarrabawa da ribar dillalai da aka ƙara a kan sabon farashin matatar.

Majiyoyi daga masana’antar sun bayyana cewa farashin ₦699 da ake sayarwa a baya wani shiri ne na ɗan lokaci da Matatar Dangote ta yi domin rage raɗaɗin farashi ga masu amfani da fetur a lokacin bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara. Da zarar wannan lokaci ya wuce, matatar ta ce sabon farashin na nuni da komawa matakin kasuwa da zai iya ɗorewa.

Wannan ci gaba na nuna irin tasirin da Matatar Dangote ke da shi a kan farashin fetur a cikin gida, musamman ganin yadda ’yan kasuwa masu zaman kansu da manyan masu rarrabawa ke ƙara dogaro da man da ake tacewa a cikin ƙasa maimakon shigo da shi daga waje.

Masu nazarin kasuwa sun lura da cewa, duk da cewa ƙarin farashin na iya ƙara wa masu amfani da fetur nauyi, tace mai a cikin gida na taimakawa wajen rage dogaro da canjin kuɗaɗen waje, kuɗaɗen shigo da mai, da kuma rashin tabbas a harkar samar da man fetur — matsalolin da a baya suka haddasa hauhawar farashi mai tsanani.

Kamfanin MRS, wanda ke daga cikin manyan abokan hulɗar Matatar Dangote a ɓangaren kasuwancin ƙasa (downstream), ya zama ɗaya daga cikin manyan wuraren sayar da fetur da Dangote ya samar a faɗin ƙasar, lamarin da ya sa farashinsa a famfo ke zama abin dubawa wajen tantance martanin kasuwa ga sauye-sauyen farashin da matatar ke jagoranta.
Gwamnatin Tarayya ta jaddada cewa an saki farashin fetur gaba ɗaya daga tsoma bakin gwamnati, inda aka bar masu tace mai da ’yan kasuwa su ƙayyade farashi bisa yanayin kasuwa, kuɗaɗe da kuma gasa.

Yayin da ƙarin matatun mai na cikin gida ke ƙara ƙarfin samarwa, masu ruwa da tsaki sun ce yanayin ƙayyade farashi zai ƙara dogaro da yanayin samar da mai a cikin ƙasa, maimakon bin farashin shigo da mai daga kasuwannin ƙetare.